Da Ɗuminsa: Ƴan Fashi Sun Kai Hari Banki, Sun Kashe Jami'in Ɗan Sanda, Sun Sace Maƙuden Kuɗi

Da Ɗuminsa: Ƴan Fashi Sun Kai Hari Banki, Sun Kashe Jami'in Ɗan Sanda, Sun Sace Maƙuden Kuɗi

  • Mutanen garin Iragbiji a jihar Osun sun hadu da tashin hankali sakamakon yan fashi da suka afka wani banki da ofishin yan sanda a garin
  • Wani dan sanda ya yi kokarin dakile harin ya riga mu gidan gaskiya yayin da bata garin suka sace makuden kudi
  • Da ya ke martani kan lamarin, kakakin yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, ya ce a tura karin jami'an yan sanda zuwa yankin

Osun - Yan fashi sun afka wani bankin zamani a Iragbaji, hedkwatar ƙaramar hukumar Boripe, a jihar Osun, a ranar Talata, sun kashe ɗan sanda.

Daily Trust ta ruwaito cewa wani mazaunin garin ya ce yan fashin sun kuma kai hari ofishin ƴan sanda da ke unguwar.

Da Ɗuminsa: Ƴan Fashi Sun Kai Hari Banki, Sun Kashe Jami'in Ɗan Sanda Da Ya Yi Musayar Wuta Da Su
Taswirar Jihar Osun. Hoto: Vanguard
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Tsohon Saurayi ya aikewa Ango tsaffin hotunan amaryarsa kan ta tuba, aure ya mutu

A cewar shaidan ganin na ido, yan fashin sun kuma kai hari ofishin yan sanda inda suka kashe dan sanda da ya yi musayar wuta da su.

Yan fashin da suka shafe kimanin minti 30 suna fashin sun sace kudade daga bankin da ke kusa da fadar basarake, Oba Abdulrosheed Olabomi.

Kakakin yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, ya ce an tura wasu jami'an yan sandan su taimaka wa na yankin.

A baya bayan nan, an kai wa wani bankin zamani hari a kusa da Iragbaji, sun sace kuɗi suka bindige dan sanda.

'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro 17 yayin harin Sokoto, Ɗan Majalisa

A wani labarin daban, dan majalisar jihar Sokoto mai wakiltar Sabon Birni ta Arewa, Aminu Gobir, ya ce an kashe jami'n tsaro 17 yayin harin da aka kai kauyen Dama a jihar, Premium Times ta ruwaito.

Premium Times ta ruwaito cewa an kashe sojoji da dama yayin da wasu suka tsere sakamakon harin da aka kai musu a sansaninsu da ke wani makaranta a kauyen.

Mista Gobir ya ce jami'an tsaron da aka kashe akwai sojoji tara, yan sanda guda biyar da kuma jami'an hukumar tsaro ta NSCDC guda uku.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel