Ana zargin mutum shida sun hallaka yayinda Soji da yan sanda suka budewa yan Shi'a wuta
- Sakataren kungiyar daliban Shi'a yace an kashe musu mutum shida
- Ya Zargi jami'an tsaron da tafiya da gawawwakin wadanda aka kashe
- Yan Shi'a sun yi muzaharar Arba'in a birnin tarayya Abuja
Abuja - Harbe-harben bindiga akan babban titin Kubwa kusa da Gwarinpa Estate ranar Talata yayinda jami'an tsaro sukayi kicibis da mabiyar akidar Shi'a masu zanga-zanga.
Ana zargin cewa mutum shida sun hallaka yayinda wasu sun jigata.
An zargi jami'an tsaron da budewa masu zanga-zangan wuta yayinda suka muzaharar Arba'in.
Sakataren daliban Zakzaky, Abdullahi Musa, bayyanawa Sahara Reporters cewa jami'an tsaro sun yi awon gaba gawawwakin.
Yace:
"Kawai harbin mutane sukeyi. Yanzu haka da nike magana an kashe mutum shida. Kai har sun yi awon gaba da gawawwakin."
Mambobin kungiyar shi'ar sun fito ranar Alhamis domin muzaharar cikar ranaku 40 da bikin jimamin ranar kisan Imam Husseini, jikan Manzon Allah (SAW) wanda aka kashe ranar 10 ga Muharram.
Sojoji Sun Yi Wa Mata 'Yan Shi'a Duka a Abuja, Sun Kama Wasu Da Dama
Sojoji sun yi wa wasu mata 'yan kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN) da aka fi sani da shi'a duka a hanyar Abuja zuwa Kaduna a safiyar ranar Talata, Daily Trust ta ruwaito.
Sojojin da suka kafa shinge a wani wuri a babban titin sun tare wani mota da ke dauke da matan.
Nan take bayan fitowarsu daga motar, sojojin suka yi wa matan bulala tare da haurin su.
Daga bisani aka tafi da su cikin wani mota da aka yi parkin din ta a gefe.
Asali: Legit.ng