Sarkin Gargajiya a jihar Osun ya gina makaranta a masarautarsa don karatun yara kyauta

Sarkin Gargajiya a jihar Osun ya gina makaranta a masarautarsa don karatun yara kyauta

  • Sarki Adedokun Omoniyi Abolarin ya gina kyakkyawar makaranta a kauyensa dake jihar Osun
  • An sanyawa sunan makarantar Abolarin College Oke-Ila, Orangun
  • Sarkin wanda shi kansa Malami ne a makarantar yace 'yayan talakawa kadai za'a dauka

Wani Sarkin Gargajiya a jihar Osun, Oba Adedokun Omoniyi Abolarin ya gina makaranta mai kyau domin jin dadin al'ummar masarautarsa marasa galihu.

Sarkin ya gina wannan makaranta ne da kudin kansa kuma dalibai na iya zuwa suyi karatu kyauta ba tare da sun biya kudin makaranta ba.

A makarantar mai suna, Abolarin College, abun da ake bukata ga dalibai shine kawai ya kasance dan talaka, za'a bashi komai da yake bukata don karatu.

Wani mai suna Ayandiji Aina ya daura bidiyo a shafinsa na Facebook inda ya yabawa kokarin sarkin.

Read also

'Yan fashi sun afka wa coci domin sace kudi, sun daba wa mai gadi wuka a Abuja

Ya kara da cewa Sarkin da kansa yana karantar da daliban makarantar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sarkin Gargajiya a jihar Osun ya gina makaranta a masarautarsa don karatun yara kyauta
Sarkin Gargajiya a jihar Osun ya gina makaranta a masarautarsa don karatun yara kyauta Photo Credit: Every Nigeria, Ayandiji Aina
Source: Facebook

Source: Legit

Online view pixel