Buɗadɗiyar wasiƙa zuwa ga Sheikh Ahmad Gumi, Alhaji Khalid Muhammad Maiflour

Buɗadɗiyar wasiƙa zuwa ga Sheikh Ahmad Gumi, Alhaji Khalid Muhammad Maiflour

Tsokacin Edita: Dukkan abubuwan da zasu karanta a wannan rubutu ra'ayin marubucin ne ba ra'ayi Legit.ng Hausa ba.

Amincin Allah ya tabbata gare ka tare da gaisuwa da girmamawa irin ta addinin Muslunci.

Na rubuto wannan wasiƙar ne domin ina son fahimtar da kai wasu abubuwa.

Sanannen abu ne, kai mutum ne mai mutunci, ɗan mai mutunci kuma jikan mai mutunci. Ganin kuwa wannan matsayi na kai kan ka, mahaifin ka da kakan ka yasa na ga ya kamata ka dinga taka tsan-tsan da kalamai da za su riƙa fita daga bakin ka.

A lokuta da dama, maganar ka ta fi takobi kaifi. Dalilin da yasa zan tunatar da kai faɗin Annabi S. A. W, "Ka faɗi alkhairi ko ka yi shiru". Hadisi ne wanda na san ka fi ni sani.

Read also

'Yan bindiga sun kashe mutane biyu, sun yi garkuwa da malami a Kaduna

Sau da yawa na kan yi mamakin maganganun ka kan 'yan fashin daji da suka addabe mu. A Wannan lokacin da gwamnati ta koro aikin ganin bayansu tare da samun galaba, ƙarfin guiwa ta ke buƙata ba suka ba.

A kan sulhu da kake ta batun a yi da su, sau nawa za a yi sulhu da miyagun nan?

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da kan ka, ka zauna sulhu da su, sama da watanni 5 da suka gabata amma babu sakamakon da muka gani. Sakamakon da mu ke son gani kuwa shi ne, su dawo cikin jama'a tare da tuba daga ɓarna. Hakan shi ne kaɗai zai nuna mana sulhun ta yi amfani.

Ina da tabbacin ka san ƙoƙarin da gwamnatin jihar Zamfara da ta jihar Katsina ke yi wurin sasanci da ƴan fashin daji. Babu inda aka samu nasara face gani da suka yi kamar suna da wani ƙarfin iko.

Read also

Daga 1 ga watan Oktoba matsalolin Najeriya za su kau, inji hasashen wani Fasto

Har ila yau, sau nawa aka yi sasancin da su, kuma aka sake kama su dumu-dumu da hannu cikin ɓarnar?

Tabbas Allah mai yawan gafara ne, balle mu bayinsa. Amma kuma Ubangiji na kaunar "Taubatan Nasuha".

Ya Sheikh tunanin da ke yawan zuwa min shi ne, rayukan waɗannan ƴan ta'addan sun fi na dukkan ƴan Najeriya ne a wurin ka? Ko kuma abinda ke tsakanin ka da gwamnati tsananin shi ya rufe maka ido, ko kuwa son da kake wa ƴan ta'addan ne ya rufe maka ido yasa ka ke ganin zaluntar su a ke yi?

Ya Sheikh, ko dai wutar su ce bata ƙone ka kamar yadda ta ƙone mu, shiyasa kake nuna tamkar ana cutar da su?

Amma kuma na kan tuna cewa, tsatson ka jihar Zamfara ce, wacce babu shakka ta na daga cikin jihohin da suka fi fuskantar wannan al'amarin na rashin tsaro.

A gaskiya wutar ƴan fashin daji ta ƙone ni. Ta taɓa ƴan uwana na jini, ta taɓa ƴan uwana na Musulunci, ka ga kuwa iyakar taɓawa da za ta yi min kenan.

Read also

Akwai yuwuwar dan siyasan Najeriya da U.S., UK ke tuhuma ya zama gwamna

Na rasa ƴan uwa na jini sama da goma. An kashe wasu har a cikin gidajensu, wasu a kan hanya, wasu kuwa sace su aka yi kuma aka ƙarba kudaden fansa. Hatta noma akwai lokutan da ya nemi ya gagaremu a yankunan kananan hukumomin Faskari, Sabuwa da Ɗandume.

Ƙauyukanmu sun yi sulhu da ƴan fashin nan amma hakan bai haifar da ɗa mai ido ba.

Ya Sheikh, ka ji irin wutar da ta ƙona ni daga wadannan miyagun ƴan bindigan.

Don haka ina rokon ka da ka kame bakin ka ko kuma ka yaba wa gwamnati a kan wannan matakin da ta dauka a matsayin ka na mai tace gaskiya komai ɗacin ta, a matsayin ka na mutumin da al'umma ke saurara, ba na Najeriya kaɗai ba, za mu iya cewa na duniyar Musulunci.

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu

Alhaji Khalid Muhammad Maiflour

Source: Legit.ng

Online view pixel