An damke wasu mata masu kaiwa yan bindiga man fetur a jihar Katsina
- Bayan kulle tituna da datse layukan waya, wasu na kaiwa yan bindiga abinci
- An damke wata tare da yaranta suna kaiwa yan bindiga man fetur
- Wannan shine karo na biyu da za'a damke irin wadannan mutane wannan makon
Katsina - Hukumar yan sanda a jihar Katsina ranar Alhamus ta damke wasu mata uku da ake yiwa zargin kaiwa yan bindiga man fetur cikin daji a jihar.
Kakakin yan sandan jihar, SP Gambo Isah, a hira da manema labarai a Katsina, ya bayyana matan uku; Dija Umar, 50; Ummah Bello, 45; da Nusaiba Muhammad, 16 yan unguwar Malali, a cikin Katsina.
Kakin yan sandan yace an damke su ne a titin Katsina zuwa Jibiya, rahoton Premium Times.
Yace:
"Wasu yan sanda sun damkesu yayin sintiri a hanyar Katsina-Jibia, suna biye da man fetur cikin jakunkuna, wanda ake zargin yan bindigan dake cikin dajin Jibia zasu kaiwa."
"Yayin bincike, Matan sun bayyana hukumar cewa lallai sun aikata laifin... Ana cigaba da bincike."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An damke masu kaiwa yan bindiga kayan abinci da man fetur a jihar Katsina
A bangare guda, hukumar yan sandan jihar Katsina ta damke mutum biyar da ake zargin suna kaiwa yan bindiga man fetur da kuma mutum guda dake kai musu burodi a jihar.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ga manema labarai ranar Talata, a jihar Katsina.
Wadanda aka kama suna kaiwa yan bindiga man fetur sun hada da Isah dan garin Maradi, da wani dan garin Magamar Jibia a mota kirar 18 ga Satumba, 2021 dauke da man fetur.
Asali: Legit.ng