A fara biyan matan aure kudin albashin zaman gida: Kotu ta yanke hukunci
- Kotu ta kasar Kenya ta baiwa matar da ta sayar da gidan miji bayan sun rabu gaskiya
- Alkalin kotun tace zaman gida sana'a ne mai zaman kansa saboda haka ba zai yiwu ayi watsi da mata ba bayan mutuwar aure
- A cewarta, daukar cikin watanni 9 daidai yake da aiki.
Kenya - Wata kotu dake zaune a kasar Kenya ya yanke hukuncin cewa aikin zaman gida tare da kula da yara sana'a ne mai zaman kansa kuma ya cancanci a rika biyan mutum albashi.
Alkali Matheka, ta yanke hakan ne a shari'ar da tayi kan lamarin dukiya tsakanin mata da miji, rahoton Jaridar EyeGambia.
An shigar da karar wata mata da ta sayar da gidansu kuma ta bukaci a raba kudin daidai bayan mutuwar aurensu.
Ta yi watsi da maganar da matan aure basu bada gudunmuwa na kudi saboda suna zama a gida.
A cewarsa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Namiji zai iya fita daga gida yana turo kudi yace gida mallakinsa ne amma matar ce ke kula da gidan da kuma yara."
"Sai kuma ya bude baki yace matarsa bata aiki kuma bata bada gudunmuwar komai."
Alkalin ta kara da cewa bai dace matar aure tace ba tada sana'a ba saboda ayyukan da take yi a gida kadai sana'a ne mai zaman kansa, kuma idan mutum na ganin cewa ba haka bane, ya nemo wani da zai yi masa.
Ta kara da cewa kula da yara aiki ne mai zaman kansa, hakazalika girki da aikace-aikacen gida.
Saboda haka, ya kamata a rika la'akari da hakan ba kawai a rika yiwa matan aure kallon marasa aiki ba kuma idan aure ya mutu ayi watsi da su.
A cewarta, daukar cikin watanni 9 daidai yake da aiki.
Tsoho mai shekaru 84 da ya bar gida tsawon shekaru 47 ya dawo, ya nuna ɓacin ransa don matansa 2 sun sake aure
Wani tsoho mai shekaru 84, Peter Oyuk ya sha mamakin yadda matan sa 2 suka sake aure bayan ya yi tafiya tsawon shekaru 47.
Kamar yadda LIB ta ruwaito daga The Standard, mutumin ya bar kauyen Makale dake Malava bangaren Kakamega a shekarar 1974 lokacin yana da shekaru 37.
Ya sanar da iyalan sa cewa ya tafi neman arziki don tallafa wa matan sa 2 da yaran sa 5 duk da dai bai sanar da su lokacin da zai dawo ba.
Asali: Legit.ng