Zaben 2023: Abin da ya sa PDP ta yarda ta sake ba ‘Dan Arewa tikitin Shugaban kasa

Zaben 2023: Abin da ya sa PDP ta yarda ta sake ba ‘Dan Arewa tikitin Shugaban kasa

  • Kwamitin Ifeanyi Ugwuanyi zai bada shawarar yadda za a raba kujerun PDP
  • Ana zargin daga bangaren Kudu za a fito da sabon shugaban jam’iyya na kasa
  • Sannan za a ba ‘Dan Arewa tikitin takarar shugaban Najeriya a zabe mai zuwa

Enugu - Yayin da jam’iyyar PDP ta ke shirin gudanar da zaben shugabanninta, an dauki matsayar kai kujerar shugaban jam’iyya na kasa zuwa yankin kudu.

Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa an kuma yarda a ba ‘dan Arewa tikitin shugaban kasa a 2023.

Sai dai shugaban kwamitin rabon mukamai na jam’iyyar PDP, Gwamnan Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi, ya ki yin bayanin yadda aka raba kujerun NWC.

Rahoton yace gwamnoni 12 daga cikin 13 da PDP take da su sun yarda a bar kujerar shugaban jam’iyya a yankin Kudu, inda Prince Uche Secondus ya fito.

Read also

Ba za mu tsayar da shugaba daga wata shiyya ba, kwamitin PDP ya magantu kan rabon kujerar shugaban kasa a 2023

Wike ya fita zakka

Wannan karo ana so shugaban jam’iyyar hamayyar ya fito daga Kudu maso yammacin Najeriya. Gwamna Nyesom Wike ne kurum yake da ra’ayi akasin haka.

Shugaban PDP na kasa
Tsohon Shugaban PDP, Prince Uche Secondus @PDPNigeria
Source: Twitter

Gwamnan Ribas ya yi kokarin karkato da ra’ayin kwamitin Ugwuanyi ya bar kofar neman kujerar shugaban jam’iyya a bude, ta yadda ‘yan Arewa za su iya nema.

Idan da kwamitin ya karbi shawarar, dole jam’iyyar adawar ta kyale kofa a bude wajen neman takarar shugaban kasa a 2023, ta yadda kowa zai iya neman tuta.

Wata majiya tace Gwamna Wike ya kawo wannan ne domin yana da burin zama shugaban kasa.

Ba za ta sabu ba

Wani gwamnan Arewa ya yi kokarin yi wa jam’iyyar PDP bayanin illar a tsaida ‘dan takarar shugaban kasa daga jihohin kudancin Najeriya a zabe mai zuwa.

Read also

ADC ta yi wa manyan Arewa kaca-kaca saboda kalamansu kan yiwuwar cigaba da rike mulki

Wani tsohon Minista a gwamnatin Goodluck Jonathan, wanda ya na cikin ‘yan majalisar NEC, ya yi magana a kan abin da ya sa PDP ta ki tsaida magana daya.

Jigon jam’iyyar yace akwai bukatar PDP ta saurara tukun, ta ga gudun ruwan APC kafin ta bayyana matsayar ta, domin ana sa ran Kudu APC za ta kai takara.

Takarar 2023

A jiya Ministan gidaje da ayyuka na kasa, Raji Babatunde Fashola, ya nesanta kansa da wasu fastocin takarar shugaban kasarsa da suke yawo a kafafen sadarwa.

Ministoci sun yi watsi da kungiyoyin da ke masu shisshigi, suna masu kamfe tun yanzu.

Source: Legit.ng

Online view pixel