2023: Fashola ya yi magana kan rade-radin tsayawa takarar Shugaban kasa da Zulum

2023: Fashola ya yi magana kan rade-radin tsayawa takarar Shugaban kasa da Zulum

  • Babatunde Fashola ya tanka fastocin yakin neman zabensa da suka fara yawo
  • Ministan yace bai da hannu a wadannan hotunan da suka fara karade shafuka
  • Shi ma Godswill Akpabio ya barranta kansa da masu yi masa yakin zaben 2023

Abuja - Ministan gidaje da ayyuka na kasa, Raji Babatunde Fashola, ya nesanta kansa da wasu fastocin takarar shugaban kasarsa da suke yawo a kafafen sadarwa.

Jaridar Punch tace Ministan ya fito ya yi magana a ranar Lahadi, 26 ga watan Satumba, 2021, ta bakin hadiminsa Hakeem Bello, yace bai san da zaman fastocin ba.

Mai taimaka wa tsohon gwamnan wajen sadarwa, Bello, yace Raji Babatunde Fashola bai da wata dangataka da kungiyar Nigeria Project 2023 da ke yin wannan aikin.

Kara karanta wannan

An kama ma’aurata kan kashe dansu tare da binne shi cikin sirri saboda ‘rashin ji’

Hotunan sun nuna tsohon gwamnan na Legas zai nemi takarar shugaban kasa a 2023, yayin da Farfesa Babagana Zulum zai tsaya masa a matsayin mataimakinsa.

Jawabin da Ministan ya fitar

“Ofishin mai girma Ministan gidaje da ayyuka, Babatunde Fashola, ya yi kira ga mutanen da suka san abin da ya dace, suyi watsi da gayyatar da wasu kungiyoyi da sunan The Nigeria Project 2023, suke yi, suna yi wa Ministan da gwamnan Borno yakin takara a zaben 2023.”
2023: Fashola da Zulum
Hotunan takarar Fashola da Zulum Hoto: www.ripplesnigeria.com
Asali: UGC

“An cika kafofin sadarwa na zamani a karshen makon da ya wuce da hotunan Mai girma Minista da gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa da kuma mataimakinsa, a karkashin wata jam’iyyar da ba a ambata ba.”

Abin da ya sa Minista ya tanka su

Kara karanta wannan

ADC ta yi wa manyan Arewa kaca-kaca saboda kalamansu kan yiwuwar cigaba da rike mulki

TheEagle ta rahoto Ministan yana cewa abubuwa biyu suka sa ya kula masu yada wadannan hotuna.

“Na farko saboda a amsa tambayar da mutane masu daraja da-dama suke yawan yi, ko an tuntubi Ministan kafin wannan kungiya ta fara abin da ta ke yi, da cewa a’a.”
"Abu na biyu shi ne, a matsayinsa na daya daga cikin manyan APC, Ministan da jam’iyya ba su san da zaman wannan kungiya ta The Nigeria Project 2023 ba."

Rahoton yace shi ma Ministan harkokin Neja-Delta, Sanata Godswil Akpabio ya wanke kan shi daga ‘yan riga malam masallaci da suke yi masa yakin zaben 2023.

NNPC ta na kashe kudi wajen harkar zabe?

A makon da ya gabata ne wani rahoto ya fito inda aka zargi kamfanin mai na kasa watau NNPC da bada kimanin Naira Biliyan 500 domin a samu nasara a zaben 2019.

Mai magana da yawun bakin NNPC yace wadannan zargin ba gaskiya ba ne. Manyan jam'iyyun kasar nan na PDP da APC sun yi gum a game da wannan zargi mai nauyi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Neja ya dakatad da zaben sabon Sarkin Kontagoran kan zargin murdiya

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng