Dokar hana fita ta IPOB: Batagari sun bankawa motar kayan miya wuta a Enugu

Dokar hana fita ta IPOB: Batagari sun bankawa motar kayan miya wuta a Enugu

  • Har yanzu kungiyar IPOB na hana mutan gari sararawa kowace ranar Litinin
  • Yan kungiyar sun kafa dokar hana fita kowace Litinin har sai an sako shugabansu Nnamdi Kanu
  • A yau an kona dukiyar dubban nairori a jihar Enugu

Enugu - Wasu batagari sun bankawa motar dake dauke da kayan miya wuta a jihar Enugu ranar Litinin bayan kungiyar rajin kafa kasar Biyafara IPOB ta kafa dokar hana fita.

Bisa hotunan da suka yadu a kafafen sadarwa, motar na dauke da tumatur, kubewa, da sauran kayan abinci.

Daily Trust ta ruwaito cewa an bankawa wannan mota wuta ne a tashar Edem, Ibeagwa, karamar hukumar Enugu ta yamma.

Jama'an gari suka kira jami'an kwana-kwana wadanda suka kashe wutar.

Wani mai idon shaida ya bayyana cewa:

"Wannan babbar asara ce da bai kamata ace ta faru ba da mutanenmu sun yi tunani ."

Read also

Tattalin Arzikin Arewa Maso Gabas Yana Daf Da Durƙushewa, NPYA Ta Yi Gargaɗi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukumar yan sandan jihar tace bata kama kowa ba har yanzu cikin wadanda suka aikata wannan aika-aika, amma dai an kaddamar da bincike.

Dokar hana fita ta IPOB: Batagari sun bankawa motar kayan miya wuta a Enugu
Dokar hana fita ta IPOB: Batagari sun bankawa motar kayan miya wuta a Enugu DailyTrust/Vantage
Source: UGC

An gano matsugunin gidan rediyon Nnamdi Kanu da yake tunzura tsageru

Shekaru da yawa kenan 'yan Najeriya ke neman sanin inda 'Radio Biafra', cibiyar rediyon kafar intanet wanda ke watsa ajandar 'yan haramtacciyar kungiyar IPOB take.

Jiya, gidan talabijin na CNN, ya gano wani titi mai cike da ganye a Peckham, kudu maso gabashin London, adireshin kungiyar ta IPOB kenan.

Gidan talabijin na CNN ya bayyana wurin a matsayin wurin da ke kusa da birni, yana mai cewa wannan wuri ne da ba a zata ba ga gidan Rediyon Biafra.

Mazi Nnamdi Kanu ya kafa haramtacciyar kungiyar IPOB a 2012 inda kuma ya kafa Rediyon Biafra a 2009. An kirkiro kungiyar ne domin maido da fafutukar kafa kasar Biafra mai cin gashin kanta.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel