Da duminsa: Gwamnatin Kaduna ta tabbatar barkewar rikici a jihar, an kashe mutum 34
- Gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa'i ya yi Alla-wadai da harin da aka kaiwa mutane Kaura
- An tabbatar da mutuwar akalla mutum 34 kuma an kona gidaje
- El-Rufa'i yayi alkawarin biyan kudin jinyan wadanda aka jikkata
- An damke mutum biyu cikin wadanda ake zargi da aikata wannan abu
Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar labarin kisan mutane talatin da hudu da yan bindiga sukayi a karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna ranar Lahadi.
Mun kawo muku cewa wasu batagari sun kona gidaje a kauyukan Madamai da Abun dake karamar hukumar Kaura a jihar Kaduna.
Kwamishanan tsaro da lamuran cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya saki jawabi ranar Litinin, 27 ga Satumba, 2021.
A cewarsa, kawo yanzu mutum 34 aka tabbatar da an kashe yayinda Sojoji suka kashe wutar daka cinnawa gidaje.
Yace:
"Sojoji sun garzaya wajen kuma suma yan bindigan suka bude musu wuta, amma daga baya suka gudu da suka ji wutan annaru."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Sun kona wasu gidaje a kauyen. Sojoji sun kashe wuta a gidaje uku, kuma sun ceto mutane shida."
"Kawo yanzu dai mutum 34 aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon harin. An garzaya da sauran da suka jigata asibiti a jihar Plateau."
Gwamnan Kaduna ya yi alhinin abinda ya faru, yayi alkawarin biyan kudin jinyan wadanda ke asibiti
Samuel Aruwan ya bayyana cewa gwamna Nasir El-Rufa'i na jihar ya yi Alla-wadai da wannan abu.
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta dauki nauyin jinyar wadanda suka jikkata kuma suka jinya a asibiti yanzu.
Yace:
"Gwamnan El-Rufa'i ya bayyana cewa gwamnatin jihar zata dauki nauyin kudin jinyar wanda suka samu raunuka."
Dan garin ya bayyana abinda ya gani
A cewar tsohon shugaban gamayyar matasan Kaura, Derek Christopher, yan bindigan sun dira garuruwan ne misalin karfe 5 na yammacin Lahadi suka bude musu wuta, rahoton Daily Trust.
A cewarsa:
"An garzaya da wasu asibiti don jinyarsu."
Legit tayi yunkurin tuntubar Kakakin hukumar yan sanda a jihar Kaduna, ASP Muhammad Jalige, amma bai daga wayarsa ba.
Asali: Legit.ng