Yadda Buhari da Jonathan suka yi amfani da biliyoyin kudin NNPC wajen samun nasarar zabe

Yadda Buhari da Jonathan suka yi amfani da biliyoyin kudin NNPC wajen samun nasarar zabe

  • Ana zargin NNPC ta bada biliyoyi domin lashe zabukan 2015 da 2019 a Najeriya
  • Wani tsohon ma’aikacin BP yace kudin da ya bada sun shiga harkar zaben 2019
  • NNPC ta musanya wannan zargi, kungiyoyi sun bukaci ayi bincike kan lamarin

Nigeria - Wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun bukaci a binciki zargin cewa NNPC ta bada kudi wajen lashe zabukan shekarar 2015 da kuma 2019.

Bloomberg ta rahoto cewa ana zargin an yi amfani da kwangilolin kamfanin wajen cin nasara a manyan zabukan da aka yi a Najeriya na 2015 da na 2019.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan ne suka gwabza a wadannan zabuka da aka yi, kuma suka amfana da kudin.

Kara karanta wannan

ADC ta yi wa manyan Arewa kaca-kaca saboda kalamansu kan yiwuwar cigaba da rike mulki

Wani tsohon ma’aikacin kamfanin man kasar Birtaniya, BP Plc, ya tona cewa wasu $300,000 da $900,000 da aka biya a 2014 da 2018 sun shiga harkar zabe.

Shugaban kungiyar CISLAC, Auwal Musa Rafsanjani ya yi Allah-wadai da yadda kamfanin man kasar yake karkatar da kudin al’umma wajen lashe zabuka.

Rafsanjani wanda shi ne shugaban Transparency International (TI) a Najeriya yace sun dade suna kiran a rika hukunta duk masu amfani da kudi wajen zabe.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari da Jonathan
Jonathan da Buhari Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

“Zaben 2019 da ya wuce ya nuna yadda aka yi amfani da dukiyar al’umma domin wasu tsirarun mutane su lashe zabe, kuma ba a hukunta su ba.”
“Akwai hujjoji masu karfi da ke nuna yadda wasu jami’an NNPC ke da hannu dumu-dumu, amma ba ayi komai domin a hana taba kudin kasa ba.”

Jaridar ta rahoto Rafsanjani yana cewa za a sake maimata irin haka a zabukan 2023 domin babu wani yunkuri da ake yi na tsabtace harkar zabe a Najeriya.

Kara karanta wannan

Karya ake yi, ba mu ce mun yi nadamar zaben Buhari a 2015 ba inji Kungiyar Dattawan Arewa

Jonathan Zarembok wanda ya yi aiki da BP yace makudan kudin da ya biya biya domin samun kwangila a NNPC ya tafi ne wajen yadda za a ci zaben 2019.

Da jaridar ta tuntubi NNPC, kakakinta, Garbadeen Muhammad, ya karyata wadannan zargi. Haka zalika jam’iyyun PDP da APC duk sun yi gum a kan batun.

Super Tucano suna hanya

A ranar Juma'ar nan ne Muhammadu Buhari ya bayyana cewa sojojin saman Najeriya za su mallaki karin jiragen Super Tucano da wasu manyan jirage.

Muhammadu Buhari ya na ganin wadannan jiragen yaki za su zama dodon ‘Yan bindiga da ‘Yan ta’adda

Asali: Legit.ng

Online view pixel