Da Ɗuminsa: Attajirin Duniya Elon Musk Da Grimes Sun Rabu Shekara Ɗaya Bayan Haihuwar Ɗansu Mai Suna X Æ A-Xii

Da Ɗuminsa: Attajirin Duniya Elon Musk Da Grimes Sun Rabu Shekara Ɗaya Bayan Haihuwar Ɗansu Mai Suna X Æ A-Xii

  • Elon Musk, mai kamfanin Space X da Tesla ya sanar da cewa sun rabu da Grimes, mahaifiyar dansa X Æ A-Xii
  • Mr Musk bai bayyana abin da ya yi sanadin rabuwarsu ba amma ya ce har yanzu suna kaunar juna kuma suna ganawa
  • Grimes, jarumar Fim ba ita bace ta fara haifawa Musk da, kafin ita ya yi aure har sau biyu kuma matarsa da farko ta haifa masa 'ya'ya 5

Amurka - Shugaban kamfanin Tesla da Space X, Elon Musk da budurwarsa, mawakiya, Grimes sun rabu bayan shafe shekaru uku tare, The Guardian ta ruwaito.

Attajirin na duniya ya shaidawa Page Six cewa shi da Grimes 'sun dan raba jiha'.

Da Ɗuminsa: Attajirin Duniya Elon Musk Da Grimes Sun Rabu Shekara Ɗaya Bayan Haihuwar Ɗansu Mai Suna X Æ A-Xii
Attajirin Duniya Elon Musk Da Grimes. Hoto: The Guardian
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Bikin tunawa da ranar 'yancin kai: FG ta yi gargaɗi mai ƙarfi ga 'yan Najeriya gabanin 1 ga Oktoba

Musk ya shaidawa jaridar cewa:

"Mun dan rabu amma har yanzu muna kaunar juna, muna ganin juna sosai kuma cikin yanayi mai kyau."
"Mafi yawanci aiki na a SpaceX da Tesla ne ke bukatar in kasance a Texas ko in tafi kasashen ketare ita kuma aikin ta ya tagayyara ne a Los Angeles."

'Yanzu tana tare da ni da jinjirin mu X a dakin da ke gefe, 'Musk yana nufin dansu mai suna X Æ A-Xii Musk da aka haifa a watan Mayun 2020.

Makonni kadan da suka shude, an gano Musk da Grimes tare a lokacin da suka hallarci wani taro, Grimes ta shiga wurin taron ita kadai ta tarar da Musk a ciki.

Bayan taron, Musk ya yi dan kwarya-kwaryar casu tare da Grimes a klub din Zero Bond, Daily Mail ta ruwaito.

X Æ A-Xii Musk ba shine kadai dan biloniyan ba. Yana da 'ya'ya biyar da tsohuwar matarsa Justine Wilson, ya kuma sake aure, suka rabu, ya sake auren jarumar film din Westworld Talulah Riley.

Kara karanta wannan

Daga 1 ga watan Oktoba matsalolin Najeriya za su kau, inji hasashen wani Fasto

A raba mu, ya ce na cika mugun ci, har rufe kicin yake yi da dare, Firdausi ta yi karar mijinta Haruna a kotu

A wani labarin daban, a ranar Litinin wata Firdausi Sulaiman mai shekaru 23 ta maka mijin ta, Haruna Haruna a gaban kotun musulunci da ke zama a Magajin Gari a Kaduna tana bukatar a raba auren su da shi saboda yadda yake dukanta kamar gangar tashe sakamakon mungun cin abincin ta.

Kamar yadda NewsWireNGR ta bayyana, a korafin da ta yi wa Kotu, Firdausi wacce take zama a Rigasa dake Kaduna ta ce har rufe kicin Haruna yake yi da dare.

Alkalin kotun, Nuhu Falalu, bayan sauraron bangarorin guda biyu, ya dage sauraron shari’ar har sai ranar 4 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel