Cikin jahilci muka yiwa yan Najeriya alkawarin canji, yanzu mun fahimci Jonathan na da gaskiya: Jigon APC

Cikin jahilci muka yiwa yan Najeriya alkawarin canji, yanzu mun fahimci Jonathan na da gaskiya: Jigon APC

  • Babban na hannun daman Buhari ya ce yanzu suka fahimci Jonathan na da gaskiya
  • Malam Faruk Adamu Aliyu ya amsa cewa cikin jahilci muka yiwa yan Najeriya alkawarin canji
  • Gwamnatin Buhari ta kai shekaru 6 shida yanzu amma yan Najeriya basu ga canjin da akayi musu alkawari ba

Abuja - Wani jigon jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Farouk Adamu Aliyu, ya bayyana cewa lallai sun jahilci halin da Najeriya ke ciki lokacin da suka yiwa yan Najeriya alkawarin canji a 2015.

Zaku tuna cewa a 2015, Jam'iyyar APC ta tsaya takarar zabe kuma ta kayar da gwamnatin PDP na shekaru 16 bisa alkawarin kawowa Najeriya canji.

Faruk Adamu Aliyu, wanda tsohon dan majalisa ne karkashin jam'iyyar ANPP ya ce rashin isasshen ilmi kan halin kasar yasa suka yiwa Najeriya wannan alkawari.

Kara karanta wannan

2023: Jiga-jigan PDP na Arewa sun dage kan tikitin takarar shugaban kasa

Ya bayyana hakan ne a shirin “Politics Today ” na tashar ChannelsTV ranar Alhamis.

Yace alkawuran da suka yiwa yan Najeriya yasa jama'a suke ganin babu cigaba duk da dimbin ayyukan da gwamnatin Buhari ke yi a shekaru 6 da suka gabata.

Cikin jahilci muka yiwa yan Najeriya alkawarin canji, yanzu mun fahimci Jonathan na da gaskiya: Jigon APC
Cikin jahilci muka yiwa yan Najeriya alkawarin canji, yanzu mun fahimci Jonathan na da gaskiya: Jigon APC Hoto: ChannelsTV
Asali: Facebook

Yace:

"Bari in amince, lokacin da muke jam'iyyar hamayya, akwai wasu abubuwan da mukayi cikin jahilci, a kuma son rai."
"Lokacin mun zagaya jihohin Najeriya domin zanga-zangar cire tallafin mai. Lokacin mun jahilci abun, wannan shine gaskiya."
"Yayinda mun dane kan kujerar mulki, sai muka fahimci Jonathan ba kuskure yayi ba, ya kamata a cire tallafi."

Faruk Adamu ya kara da cewa yanzu sun fahimci cewa Jonathan na kan hanya.

Jam'iyyar APC ta bayyana dalilin da yasa ta dage gangamin taronta na jihohi

Kara karanta wannan

Da yawa daga cikin masu sukar Buhari su kan lallaɓa Villa diɓar 'jar miya'

Jam'iyyar APC mai mulki ta bayyana cewa ta ɗage gangamin tarukanta na jihohi daga 2 ga watan Oktoba zuwa 16 ga watan Oktoba, 2021, saboda cikar Najeriya shekara 61 da samun yancin kai.

Jam'iyyar ta faɗi haka ne a wani jawabi da ta fitar ranar Alhamis, ɗauke da sa hannun sakataren kwamitin rikon kwarya na APC, sanata John James Akpanudoedehe.

A jawabin da sakataren ya fitar, APC tace:

"Saboda mu girmama bikin cikar Najeriya shekara 61 da samun yancin kai, wanda za'a yi kwana ɗaya kafin ranar taron da muka sanya da farko, shiyasa muka sanar da sabon lokaci."

Asali: Legit.ng

Online view pixel