Buhari yana so manyan Duniya su yafe wa Najeriya da wasu kasashe bashin da ake bin su

Buhari yana so manyan Duniya su yafe wa Najeriya da wasu kasashe bashin da ake bin su

  • Muhammadu Buhari ya yi jawabi a wajen taron majalisar dinkin Duniya
  • Shugaban Najeriyar ya roki alfarma wajen shugabannin kasashe a UNGA
  • Shugaba Buhari yana so a yafe bashin da ake bin kasashe masu taso wa

USA - Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya roki manyan kasashe 20 da ake da su a Duniya, suyi wa kasashe masu taso wa afuwar bashin da ake bin su.

The Nation tace Muhammadu Buhari yana so a ji tausayin kasashen da suke fama da karancin kudi.

Da yake magana a wajen taron majalisar dinkin Duniya, UNGA, Buhari ya yi kira ga kasashe masu karfin tattali su yafe bashin da suke bin kasashe irin Najeriya.

Ganin yadda annobar COVID-19 ta jefa kasashe cikin matsin lamba, Muhammadu Buhari ya nemi a yafe wa kasashe marasa karfi bashin da ya yi masu katutu.

Kara karanta wannan

Shugabancin 2023: Yakasai ya lissafa 'yan siyasa 3 na kudu da ka iya nasara a matsayin dan takarar APC

“Kasashe masu taso wa suna fama da kalubalen biyan bashi tun kafin a fara annoba (COVID-19).”
Buhari
Buhari a taron UNGA Hoto: punchng.com

“Annobar COVID-19 ya kara jawo matsalar bashi, kudin da ya kamata ayi amfani da su wajen kiwon lafiya da ayyuka sun tafi a biyan bashin da aka ci.”
“Dole in yaba da kokarin da kungiyiyoyin tattalin arziki da G20 na rage matsin tattalin arzikin kasashen da ake bi bashi, ina kira su kara kokarin.”

A gaban shugabannin Duniyan, shugaban Najeriyar ya bada shawarar a duba yadda za a dauke bashin da ke wuyan kasashen da nauyi ya yi masu yawa.

Buhari ya yi magana a kan juyin-mulki

Haka zalika a taro UNGA na 76, Muhammadu Buhari ya kira ga kasashen Duniya su tashi tsaye a kan sojojin da suke hambarar da gwamnatocin farar hula.

Kara karanta wannan

Abubuwa 7 da Shugaba Buhari ya fada a jawabin da yayi a majalisar dinkin duniya

Jaridar ta rahoto Buhari yana cewa dade wa fiye da kima da shugabannin Afrika suke yi a kan mulki ne yake jawo sojoji su kifar da gwamnatocin kasashe.

Osinbajo ya yi jawabi a Akwa Ibom

A jiya aka ji Farfesa Yemi Osinbajo ya kaddamar da gidajen Dakkada a jihar Akwa Ibom. Mataimakin shugaban kasar ya yabi kokarin gwamnan Akwa Ibom.

Osinbajo yace gwamnatin APC ta kashe N8tr wajen abubuwan more rayuwa. A cewarsa, babu gwamnatin da ta batar da kudi wajen gina tituna irin gwamnatin APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel