Ina karatu na tsawon awanni 17 a rana, Cewar matashin da ya gama Jami'a da 1st Class
- Wani matashi, Oluebube Miracle ya kammala karatunsa a jami'ar UNIZIK da CGPA 4.87
- Matashin ya bayyana irin jajircewan da yayi domin ganin cewa ya samu wannan sakamako
- Oluebube ya godewa iyaye da yan uwansa da suka taimaka masa yayinda take karatu
Oluebube Miracle Alphonsus Okoye ya zama zakaran dalibin shekarar 2020/2021 a jami'ar Nnamdi Azikiwe University, Awka (UNIZIK) inda karanci ilmin kimiyyar magunguna (Pharmacy).
Oluebube ya fito da daraja na 1 da kuma CPGA na 4.87 cikin 5.0.
Wakilin Legit.ng Franklin Onwubiko, ya tattaro cewa Oluebube ya zama abin kallo a bikin yaye dalibai da ya gudana a jami'ar.
Wannan shine Digirinsa na biyu
Okoye wanda dan asalin jihar Anambra ne ya kammala karatun Likitanci a 2014 kafin ya sake komawa makarantar domin karanta Ilmin kimiyyar magunguna.
Yanzu ya zama Dakta na kiwon lafiya kuma Dakta na magunguna.
Matashin mai shekaru 31 yanzu ya bayyana cewa ya samu nasara ne saboda jajircewarsa da kuma son zarcewa sa'anninsa.
Yace:
"Abinda ke ingiza ni shine ganin cewa na fita daban da sauran jama'a. Kawai ina son ganin nine kan gaba."
Yana karatun awanni 17 a rana
Oluebube ya bayyana cewa akwai lokutan da yakan yi karatun sa'o'i 17 a rana don ganin cewa shine zakara.
Yace ba karamin wahala ya sha wajen hada karatu da aiki ba amma duk da haka bai gajiya ba.
Gwamna Zulum ya dakatar da shugabannin makarantar da ya yi karatu yayin da ya kai ziyarar bazata
A bangare guda, gwamna Babagana Zulum ya dakatar da dukkanin shugabannin kwalejin kimiyya ta Ramat da ke Maiduguri, na tsawon watanni shida.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Zulum ya kasance dalibin kwalejin kimiyyar daga shekarar 1986 zuwa 1988. Ya sami difloma a bangaren Injinyan Noma kafin ya koma makarantar a matsayin shugaba daga 2011 zuwa 2015.
A yayin ziyarar bazata da ya kai, gwamnan ya yi mamakin ganin cewa dakunan bitar aiki da na gwaje-gwaje ba sa aiki, yayin da ‘makarantar ta mutu murus’.
Asali: Legit.ng