MURIC ta mayar da martani kan sauya shekar Fani-Kayode zuwa APC, ta bayyana abin da zai faru

MURIC ta mayar da martani kan sauya shekar Fani-Kayode zuwa APC, ta bayyana abin da zai faru

  • Kungiyar Kare Hakkokin Musulmai (MURIC) ta bayyana cewa sauya shekar tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, kyakkyawan ci gaba ne
  • Farfesa Ishaq Akintola, darakta kuma wanda ya kafa MURIC, ya bayyana wannan a cikin wata sanarwa da shi da kansa ya sa hannu
  • A cewarsa, ya kamata a ga canjin zuciyar FFK daga kusurwa mai kyau, musamman ga waɗanda ke son ci gaban Najeriya a zuciya

Lagos - Wata kungiyar kare hakkin Musulunci (MURIC), ta mayar da martani kan sauya shekar tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode zuwa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa kungiyar ta ce yan Najeriya za su samu riba sosai sakamakon ficewar Fani-Kayode zuwa APC.

MURIC ta mayar da martani kan sauya shekar Fani-Kayode zuwa APC, ta bayyana abin da zai faru
MURIC ta ce sauya shekar Fani-Kayode zuwa APC zai inganta hadin kan Najeriya Hoto: Femi Adesina.
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa darakta kuma wanda ya kafa MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce "duk da guguwar sukar da ta gaishe da matakin FFK", ficewarsa zai haifar da hadin kai a kasar.

Kara karanta wannan

Duk da yi wa Yusuf Buhari fatan mutuwa, shugaba Buhari ya yafewa Fani-Kayode

PM News ta kuma ba da rahoton cewa MURIC, ta ce ba za ta shiga cikin waɗanda suka kalli batun ta kusurwa ɗaya kawai ba, ta kara da cewa za ta yi zurfin tunani mai nisa don ba ta damar ganin dukiya mai daraja da aka ɓoye a bayan manyan duwatsu.

Sanarwar ta ce:

"Fani-Kayode mutum ne wanda ya nuna rashin goyon baya ga masu neman ballewa, masu son kawo rauwa da masu neman ballewa. Najeriya ta karkata zuwa tafarkin yaki da rugujewa sakamakon tashin hankalin kungiyoyin da yake marawa baya, a yau, FFK a sabon sansaninsa yana iya inganta hadin kan Najeriya.
“Dansa, Cif Femi Fani Kayode, a yau ya sake yin irin wannan musabaha a fadin Nija. Yakamata a duba canjin zuciyar FFK daga kusurwa mai kyau, musamman ga waɗanda ke nufin Najeriya da alheri."

Kara karanta wannan

Nan da shekaru 2 za a kammala wurin kiwon shanun jihar Kaduna na N10bn, El-Rufai

MURIC ta kuma yabawa Buhari saboda hakurin da ya yi da masu sukarsa.

Duk da yi wa Yusuf Buhari fatan mutuwa, shugaba Buhari ya yafewa Fani-Kayode

A wani labarin, Femi Adesina, hadimin shugaban kasar Najeriya kan harkokin yada labarai, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yafewa tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma babban mai sukar gwamnatinsa, Femi Fani-Kayode (FFK).

Legit.ng ta rahoto Adesina a cikin wata kasida da ya fitar a ranar Alhamis, 23 ga watan Satumba, inda yayi kira ga membobin APC da su maida takubban su kuma su karbi FFK a jam'iyyar cikin soyayya.

Ya ce FFK ba wani mummunan hali yake dashi ba, kuma duk abin da ya yi, ko bai yi ba, yana jan hankali sosai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel