Naira na da karfi, dan Najeriya zai ci ya koshi da N500, Farfesan Tattalin Arziki

Naira na da karfi, dan Najeriya zai ci ya koshi da N500, Farfesan Tattalin Arziki

  • Wani Farfesan Tattalin arziki ya bayyana matsayar Naira game da karfin darajarta
  • A bayaninsa, Yan Najeriya na cikin talauci saboda ba kowa ya mallaki sama da N500 a rana ba
  • Farfesa yace a nan gida N500 zata kosar da mutum, amma a waje ba ta da daraja

Abuja - Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin Najeriya (CIBN), Prof Segun Ajibola, ya bayyana cewa mutane su daina ruduwa da fadin darajar Naira idan aka danganata ga Dalar Amurka.

Segun ya bayyana cewa da N500, dan Najeriya zai ci ya koshi a yau.

Farfesan wanda Malamin ilmin tattalin arziki ne a jami'ar Babcock, ya bayyana hakan ne ranar Laraba, 22 ga Satumba, yayin hira a tashar NTA.

A cewarsa, darajar kudi na nuni ga karfin tattalin arzikin kasa da kuma rauninsa.

Kara karanta wannan

Daga 1 ga watan Oktoba matsalolin Najeriya za su kau, inji hasashen wani Fasto

Yace:

"Har yanzu Naira na da karfi. Da N500, dan Najeriya zai iya ciyar da kansa a yau amma idan muka danganata a Dalar Amurka ko Fam, babu abinda zaka iya yi da Fam daya a Landan, ba zaka iya sayan wani abun kirki da Dala daya ba a New York (Amurka)."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Saboda haka, akwai banbanci tsakanin darajar Naira a Najeriya da kuma darajarta a waje, idan akayi la'akari da abinda mutum zai iya saya da shi."
"Mun lura cewa Naira a yanzu na da daraja a Najeriya amma a kasar waje, akwai matsala."

Naira na da karfi, dan Najeriya zai ci ya koshi da N500, Farfesan Tattalin Arziki
Naira na da karfi, dan Najeriya zai ci ya koshi da N500, Farfesan Tattalin Arziki Hoto: Prof Segun
Asali: UGC

Amma fa N500 ba zai kosar da mutum guda a rana ba

A wata hira daban kuma da jaridar Guardian, masani tattalin arzikin ya yi fashin baki kan maganarsa inda yace N500 ba zai ciyar da mutum sau daya ba a rana guda ba.

Kara karanta wannan

Aikin wutan da ya yi sanadiyyar mutuwar Abba Kyari ya tsaya cak bayan an sa hannu

A cewarsa, yanzu sai mutum ya tanadi N45,000 a wata yaci abinda yake so a Najeriya kuma hakan yasa talauci ya yawaita.

Yace:

"Abin shine: A N500 sau daya, N1500 kullum, N45,000 a wata, kudin da dan Najeriya ke da shi ba zai isa ciyar da shi ba kuma hakan ke haifar da yawaitar talauci."

PDP ta nemi gwamnan CBN Godwin Emefiele ya gaggauta barin ofis

Jam’iyyar PDP ta bukaci gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele yayi murabus cikin gaggawa, Daily Trust ta ruwaito.

Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP na Kasa, Kola Ologbondiyan ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Alhamis 23 ga watan Satumba a Sakateriyar Jam’iyyar ta Kasa da ke Abuja.

Ologbondiyan ya ce abin koyi ne a lura cewa lokacin da Emefiele ya hau kujerar Gwamnan Babban Bankin Najeriya a 2014 darajar Naira ta kasance N164 idan aka kwatanta da dalar Amurka.

A cewar Ologbondiyan yau hannun Emefiele da APC, Naira ta durkushe zuwa kusan N600 zuwa dala, ta durkusar da tattalin arzikin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel