An damke masu kaiwa yan bindiga kayan abinci da man fetur a jihar Katsina

An damke masu kaiwa yan bindiga kayan abinci da man fetur a jihar Katsina

  • Bayan kulle tituna da datse layukan waya, wasu na kaiwa yan bindiga abinci
  • An damke wasu na kaiwa yan bindiga man fetur da suke sufuri da shi
  • Kaakin yan sandan jihar ya bayyanasu a hira da manema labarai

Katsina - Hukumar yan sandan jihar Katsina ta damke mutum biyar da ake zargin suna kaiwa yan bindiga man fetur da kuma mutum guda dake kai musu burodi a jihar.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ga manema labarai ranar Talata, a jihar Katsina, rahoton DailyTrust.

Wadanda aka kama suna kaiwa yan bindiga man fetur sun hada da Isah dan garin Maradi, da wani dan garin Magamar Jibia a mota kirar 18 ga Satumba, 2021 dauke da man fetur.

Kara karanta wannan

EFCC ta kama 'yan damfara ta intanet 30 a jami'ar KWASU

Yace:

"Hukumar ta samu nasarar damke dan shekara 50, mazaunin garin Daddara a karamar hukumar Jibia shima yana kai man fetur a motarsa Golf3."
"Hakazalika mun samu nasarar damke dan shekara 57, a Kofar Guga Quarters, yana kai man fetur."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An damke masu kaiwa yan bindiga kayan abinci da man fetur a jihar Katsina
An damke masu kaiwa yan bindiga kayan abinci da man fetur a jihar Katsina Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Bayan haka, hukumar ta damke wani dan shekara 30 daga Sabon garin MotsoMotso, a Jibiya, wanda ake zargin yana kaiwa yan bindiga labarai kuma yana kai musu burodi.

Yace:

"Bayan gargadin da shugabannin gari da jami'an tsaro ke yi masa cewa ya daina kaiwa yan bindiga burodi cikin daji, an damkesa da Burodi cikin buhu yana kokarin shiga cikin daji."

SP Isah ya kara da cewa mutumin ya amsa laifukan da yayi kuma an kaddamar da bincike.

An toshe hanyoyin sadarwa na zamani a jihar Katsina

An toshe hanyoyi sadarwa na zamani a kananan hukumomin jihar Katsina akalla 13 a yau Alhamis, 9 ga watan Satumba, 2021.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun afkawa coci ana cikin ibada, sun kashe mutum 1, sun sace 3

Wannan sabon abu ba zai rasa alaka da artabun da jami'an tsaro ke yi da yan bindiga a yankin Arewa maso yamma ba.

Kananan hukumomin da wannan abu ya shafa sun hada da Sabuwa, Faskari, Dandume, Batsari, Danmusa, Kankara, Jibia, Safana, Dutsin-Ma da Kurfi, Funtua, Bakori da Malumfashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng