Femi Fani-Kayode: Sabon 'jagwal' ne ya shigo jam’iyyar APC, PDP

Femi Fani-Kayode: Sabon 'jagwal' ne ya shigo jam’iyyar APC, PDP

  • Jam’iyyar PDP ta kwatanta Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama a matsayin dan siyasar kafar sada zumunta
  • Bayan komawar sa APC, mataimakin sakataren yada labaran PDP, Hon Diran Adeyemi ya ce FFK ba ya da wani tasiri
  • Odeyemi ya kara da jan kunnen hukumar EFCC akan janye zargin rashawar da take yi wa Fani-Kayode da sauran wadanda su ka koma APC

FCT Abuja - Jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP ta kwatanta Femi Fani-Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama a matsayin dan siyasar kafar sada zumunta.

Yayin yin tsokaci akan barin PDP da Fani-Kayode ya yi, mataimakin sakataren yada labaran jam’iyyar, Hon Diean Odeyemi ya ce babu wani tasiri da Fan-Kayode zai yi wa APC kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

‘Dan APC ya fito yana banbami, yace duk satar mutum, da ya shigo cikinsu ya zama Waliyyi

Femi Fani-Kayode: Sabon 'jagwal' ne ya shigo jam’iyyar APC, PDP
Shugaba Muhammadu Buhari, Femi Fani-Kayode, Boss Mustapha, Bello Matawalle, Mai Mala Buni. Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Yanzu ne ‘yan Najeriya zasu gane idan da gaske Buhari yake yaki da rashawa

Odeyemi ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari akan ya tabbatar da anyi adalci akan shari’ar rashawar da Fani-Kayode da sauran wadanda su ka koma jam’iyyar APC.

Ya kuma ja kunnen EFCC akan janye zargin rashawa akan Fani-Kayode da sauran su.

Odeyemi ya kara da cewa ba su taba daukar Fani-Kayode a matsayin dan jam’iyyar PDP ba, ko a garin su na Ile-Ife ko Abuja inda yake zama babu wanda ya san da shi.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, wani bangare na takardar ya zo kamar haka:

“Yanzu ne ‘yan Najeriya zasu sani idan da gaske Shugaban kasa Muhammadu Buhari dagaske yana yaki da ta’addanci.

Kara karanta wannan

APC ta gindaya wa FFK sharuddan da zai cika kafin ta gama amincewa da shi

“Yan siyasa irin Fani-Kayode da sauran su sun koma jam’iyyar APC ne musamman don su guje wa tuhumar EFCC, don haka muna jiran mu ga an dauki matakin da ya dace akan su.
“Idan har aka yi hakan, zai tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa shigar mutane APC ba shingen shari’a da EFCC bane. Idan har dagaske yana yaki da rashawa, wajibi ne a tuhumi mutum kamar Fani-Kayode wanda ake zargi da wawurar naira biliyan 2, wanda aka ware don ginin titi a filin jirgin Enugu.
“Idan aka yi hakan, za a tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ba a takura musu su shiga APC ba, sannan ba za su gujewa tuhumar EFCC ba.
“Muna kara tabbatar wa kowa cewa Fani-Kayode jagwal ne a siyasa. Bai yi rijistar zama dan PDP a ko ina ba. Ba ya da mazaba ko wata daraja, kawai ya samu damar zama minista ne saboda sa’ar rayuwa.

Kara karanta wannan

Bayan barin gidan Sheikh Pantami, an ga Fani-Kayode ya je cin abinci a gidan wani Ministan

“Muna taya APC murnar kwasar jagwalgwalo irin Femi Fani-Kayode. Kuma abin mamakin shine yadda babu wani dan APC da ya yi zanga-zanga akan shigar sa jam’iyyar su.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel