‘Dan APC ya fito yana banbami, yace duk satar mutum, da ya shigo cikinsu ya zama Waliyyi
- Jonathan Vatsa ya yi Allah-wadai da karbar Fani-Kayode a Jam’iyyar APC
- Jagoran na APC a jihar Neja yace jam’iyyarsu ta rasa inda ta sa gaba yanzu
- A cewarsa za a iya yafe wa Igboho da Kanu idan har suka shigo jirgin APC
Niger - Wani jagora na jam’iyyar APC mai mulki a jihar Neja, Jonathan Vatsa ya fito ya yi Allah-wadai da sauya-shekar da Femi Fani-Kayode ya yi daga PDP.
Jaridar Daily Post ta rahoto Jonathan Vatsa yana cewa da a ce Nnamdi Kanu da Sunday Ighoho za su shiga jam’iyyar APC, da an yafe masu laifuffukan da suka yi.
Da yake maida martani a kan shigo war da tsohon Minista Femi Fani-Kayode ya yi zuwa APC, Vatsa ya koka a kan yadda idanuwan shugabannin APC ya rufe.
Head Topics ta rahoto Jonathan Vatsa yana jawabi a garin Minna, Jihar Neja inda yace abin kunya ne a ce yau Fani-Kayode ya shigo jam’iyyar APC mai mulki.
Vatsa ya shaida wa manema labarai cewa jam’iyyar APC tana kokari ido rufe ne domin ta cigaba da mulki don haka za ta iya yayimo kowane irin ‘dan siyasa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da zarar ka tsallako APC, an yafe maka
“Ba zan yi mamaki idan Kanu da Igboho suka shigo APC ba, sai aka fito da su daga zaman kason da suke yi, sannan kuma ayi masu kyakkyawar tarba.”
“Wannan matsanancin hali ne da jam’iyyar ta samu kanta. Duk satar da mutum ya yi, da ya shigo APC, ya zama waliyyi. Abin takaici da Allah-wadai ne.”
“Wadanda suka wawuri kudi a baitul-mali sun zama gwaraza yanzu a cikin jam’iyyar APC. Komai ya damalmale. Jam’iyyar nan ta rasa inda ta sa gaba.”
A cewar Vatsa shugaba Muhammadu Buhari da duk ‘yan Najeriya sun san zargin da ake yi wa Fani Kayode na satar Naira biliyan biyu a gwamnatin PDP.2
Bayan zargin badakalar sace kudin gina titin jirgin saman Fatakwal, Vatsa yace an san rawar da tsohon Ministan ya taka a badakalar nan ta #DasukiGate.
Kila APC ta watse
An ji jagoran APC a kudu maso gabashin Najeriya, Sanata Rochas Okorocha yace ya goyi bayan Gwamnonin kudu da suke neman mulki ya bar yankin Arewa.
Tsohon Gwamnan Imo ya kuma fada wa Gwamnatin Muhammadu Buhari abin da ya dace tayi wa Nnamdi Kanu da Sunday Igboho da ke tsare a hannun hukuma.
Asali: Legit.ng