Obasanjo ya samu matsayi a AU, ya fara aiki a matsayin Jakadan zaman lafiya a kasashen Afrika
- Olusegun Obasanjo ya isa kasar Habasha a matsayin babban wakili na kungiyar AU
- Tsohon shugaban Najeriyar zai kawo karshen rikicin wasu kasashen Afrika ta gabas
- Ana fama da rashin kwanciyar hankali a Djibouti, Eriteriya, Habasha, Uganda, Sudan
Ethiopia - A Agustan 2021 ne shugaban kungiyar kasashen Afrika ta AU, ya hada Olusegun Obasanjo da aikin kawo zaman lafiya a cikin nahiyar.
Jaridar Premium Times tace tsohon shugaban kasar Najeriya zai yi kokarin tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da lumana a gabashin Afrika.
Olusegun Obasanjo ya isa birnin Addis Ababa ta kasar Habasha domin fara aikin da aka ba shi na babban jakadan kungiyar AU a kasashen da ke yankin.
Ana sa rai Obasanjo wanda yana cikin dattawan Afrika ya kawo karshen tashin-tashinan da ake yi a kasashen Afrika ta gabas inda ake fama da yawan rikici.
Wasu kasashe ake fama da rikici?
Kasashen da aka ba Obasanjo dawainiyar kawo zaman lafiya sune; Djibouti, Eriteriya, Habasha, Somaliya, Kenya, Sudan, Sudan ta kudu da kuma Uganda.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahoton yace jawabin da ya fito daga bakin shugaban hukumar AU, Moussa Faki Mahamat, yace Obasanjo zai shiga, ya fita domin kawo karshen rigingimun.
Kungiyar AU tana ganin Obasanjo yana da kware war da zai sa rigingimun yankin su zama tarihi.
“Babban wakilin zai karfafa tattauna wa da ‘yan siyasa da sauran masu ruwa-da-tsaki domin a wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.”
Tsohon shugaban kasar ya shaida wa manema labarai cewa ya isa garin Addis Ababa a ranar Talata, 21 ga watan Satumba, 2021, kuma ya ma soma aikinsa.
Tuni har Obasanjo ya zauna da shugabannin kasar Habashan da wasu jagororin AU. Sannan zai shiga gana wa da shugabanni daga Sudan, Kenya da Somaliya.
'Yan Arewa na kuka a Najeriya
A baya aka ji kungiyar dattawan Arewa tana cewa Arewa ta shiga halin ha’ula’i a yau ne saboda na ta ne yake mulki. Hakeem Baba Ahmed ya bayyana wannan.
Dr. Hakeem Baba Ahmed yace babu wani wanda zai yi wa yanki Arewacin Najeriya dole, yace Kudu za su tsaida Shugaban kasa ko an ki, ko an so a zaben 2023.
Asali: Legit.ng