Illoli 5 da ke tattare da cin namijin goro

Illoli 5 da ke tattare da cin namijin goro

Namijin goro (Garcinia kola; a kimiyyance) dan itaciya ne da ke da tasiri wajen warkar da cututtuka da dama. Sai dai duk da wannan amfani da namijin goro ke yi, yana da illoli da kan iya yiwa jiki lahani.

Ga wasu daga cikin illolin da namijin goro kan iya haifarwa ga jikin mutum da kuma lafia

1. Namijin goro kan iya haddasa kansar baki (mouth cancer): Yawan cin namijin goro kan iya jawo ciwon dajin baki ko kuma uwar hanji.

Namijin goro na dauke da sinadarin gahawa (caffeine) mai yawa, yawan gahawa a jiki kan iya kashe mutum ko ya jawo ma sa ciwon zuciya.

2. Namijin goro yana taba ido/gani (glaucoma): Cin namijin gora kadan na taimakawa ido/gani, sai dai cinsa da yawa na iya haddasa matsalar idanu. Akwai bukatar ya kula da adadin namijin goro da ya ke ci a rana.

Illoli 5 da ke tattare da cin namijin goro
Illoli 5 da ke tattare da cin namijin goro
Asali: UGC

3. Yana tunzura gudawa: Namijin goro na iya tunzura gudawa idan aka ci shi da yawa. Masana sun shawarci ma su fama da gudawa su guji cin namijin goro.

DUBA WANNAN: Wani uba ya kashe diyarsa, ya ce Allah ne ya umarce shi

4. Yana tsinka jini: Masana sun bayar da shawarar cewar ma su rauni su guji cin namijin goro saboda yana jinkirta daskarewar jini.

Kazalika an shawarci wadanda aka yiwa tiyata su guji cin namijin goro.

5. Yana kara rikicewar kwakwalwa: Akwai wasu sinadarai a cikin namijin goro da ke kara tunzura matsalar rikicewar kwakwalwa, hakan ne ya saka masana bawa ma su matsalar rikicewar kwakwalwa kauracewa cin namijin goro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel