Sojoji Sun Cafke Sajan Ɗan Sanda Da Harsasai 370 a Plateau

Sojoji Sun Cafke Sajan Ɗan Sanda Da Harsasai 370 a Plateau

  • Rundunar soji ta OPSH ta kama wani dan sanda a jihar Filato dauke da carbin harsasai 370 a ranar Alhamis
  • Ya tuko mota ne ya biyo titi sai sojojin suka dakatar da shi da abokin harkar sa a madakatar su
  • Sun samu nasarar kwace harsasan sannan da suka tsananta bincike har wiwi suka samu a wurin sa

Jihar Filato - Rundunar soji ta musamman ta Operation Safe Heaven (OPSH) ta ce ta kama wani dan sanda mai mukamin Sergeant da harsasai guda 370 a jihar Filato, Daily Trust ta ruwaito.

Jami’in hulda da jama’an rundunar, Ishaku Takwa ya bayyana hakan a wata takarda da ya saki a ranar Alhamis.

Sojoji Sun Kama Sajan Ɗan Sanda da Carbin Harsasai 370 a Plateau
Sajan Ɗan Sanda Da Sojoji Suka Kama Da Carbin Harsasai 370 a Plateau. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

'Yan sanda za su gurfanar da wata matashiya ‘yar shekara 25 da ke yi wa ‘yan bindiga leken asiri a Katsina

Kamar yadda The Cable ta ruwaito Takwa ya ce sun kama dan sandan ne a ranar Alhamis da rana a daidai kan titin anguwar Werreng dake karamar hukumar Barkin Ladi ta jihar.

Tare da wani tsoho aka kama shi

Dan sandan ya tuko abin hawar ne tare da wani dattijo mai shekaru 60 a lokacin da sojojin suka dakatar da shi.

A cewar sa:

“Da rana rundunar mu ta ci karo da dan sanda tare da wani abokin harkar sa dauke da harsasai masu carbi guda 370,” kamar yadda takardar ta zo.
“Sun adana harsasan a wata mota kirar Toyota Pathfinder jeep mai lambar rijistar LGT 772 JN.
“Asirin wadanda ake zargin ya tonu ne bayan direban ya yi yunkurin canja hanya daga matsayar sojin wuraren Werreng kan titin Barkin Ladi zuwa Jos. Sai dai motar ta ci karo da madakatar sojojin wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar daya daga cikin su."

Kara karanta wannan

Rundunar sojin saman Najeriya ta fara bincike kan barin wuta da jirgin yaki ya yi kan fararen hula a Yobe

The Cable ta ruwaito yadda Takwa ya ce da aka tsananta bincike an gano cewa direban dan sanda ne inda ya kara da cewa sun mika gawar sa ga rundunar ‘yan sanda yayin da dayan yake shan tambayoyi.

Sauran abubuwan da aka samu a hannun su sun hada da mota kirar Toyota Pathfinder, N205,000, daga, ma’ajin harsasai, tocila da wayoyi 3.

An samu katin wurin aikin sa, daurin wata hoda da ake zargin wiwi ce da wata jaka da ake zargin kayan sawan su ne.

Kakakin OPSH ya kara da cewa yanzu haka wanda ake zargin yana hannun ‘yan sanda suna kara bincike akan sa kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Kashe-Kashen Jos: CAN ta miƙa muhimman saƙo ga shugabannin musulmi da kirista a Plateau

A wani labarin daban, Kungiyar kirista ta Nigeria, CAN, a Jos, babban birnin jihar Plateau ta roki shugabannin musulmi da na kirista su dena tunzura mutane suna miyagun ayyuka, Peoples Gazette ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sojoji sun damke tsohon soja yana jigilar tulin wiwi da kwayoyi daga Ondo zuwa Jihohin Arewa

A cewar sanarwar da ta fitar a garin Jos a ranar Laraba mai dauke da sa hannun shugaban CAN, Polycarp Gana da satare Ezekiel Noam, kungiyar ta kuma yi Allah wadai da kashe-kashen da aka yi a Yalwan Zangam.

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun afka garin a daren ranar Talata sun kashe mutane masu yawa sannan suka kona gidaje da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164