Gwamna Sule: Dokar hana kiwo da wasu jihohi suka saka bata aiki

Gwamna Sule: Dokar hana kiwo da wasu jihohi suka saka bata aiki

  • Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya soki dokar hana kiwo a fili da wasu jihohi suka rattaba hannu kan ta
  • Jihohin da suka rattaba hannu kan dokar sun hada da Enugu, Rivers, Akwa Ibom, Ondo da Legas
  • Gwamna Sule ya ce dokar bata aiki don haka babu dalilin da zai sa jiharsa ta yi koyi da sauran jihohin musamman na kudu

Jihar Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce dokar hana kiwo a fili da wasu takwarorinsa suka saka a jihohinsu baya aiki.

Gwamnoni jihohin Enugu, Rivers, Akwa Ibom, Ondo da Legas duk sun rattaba hannu kan dokar, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamna Sule: Dokar hana kiwo da wasu jihohi suka saka bata aiki
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Da duminsa: Sanwo-Olu ya sa hannu kan dokar hana kiwo a fili a Legas

Gwamnonin jihohin na Kudu sun tsayar da ranar 1 ga watan Satumban 2021 a matsayin ranar da za a rattaba hannu kan dokar.

A hirar da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels, Sule ya ce ya yi imanin cewa tsarin baya aiki, rahoton Daily Trust.

Ya ce:

"Ba mu son tsarin dokar hana kiwo a fili da ake amfani da shi, abin baya aiki".
"Ba wai za mu yi abu bane domin kowa na yi game da dokar hana kiwon. Idan ka rattaba hannu kan doka kuma bata aiki, ya kamata ka dage kan dokar?"

Gwamnonin Arewa za su kafa wuraren kiwo na zamani

Amma, Sule ya ce ya yi imanin cewa irin kiwon da makiyaya ke yi a yanzu ba shine abin da ya dace ba.

Ya ce:

"Abin da dukkan gwamnonin arewa suka yarda a kai shine tsarin kiwo na yanzu ya tsufa kuma ba za a cigaba da shi ba."

Kara karanta wannan

Abinda yasa na bar PDP, gwamnonin PDP 3 da na sha alwashin ja zuwa APC, Fani Kayode

Ya kara da cewa a madadin dokar hana kiwo, gwamnatin jihar Nasarawa da gwamnatin tarayya za su amince da tsarin kiwo na kasa.

Ya yi bayanin cewa gwamnatinsa za ta samarwa makiyaya wurin kiwo guda bakwai.

A cewarsa:

"Abin da ya fi dacewa shine ka bawa mutane zabi; abu mai sauki ne gwamnatin jihar Nassarawa ta yi dokar hana kiwo cikin mako guda."

Asali: Legit.ng

Online view pixel