Bincike: Yadda tsohon mataimakin gwamnan CBN, Mailafia ya rasu, Jami'ai

Bincike: Yadda tsohon mataimakin gwamnan CBN, Mailafia ya rasu, Jami'ai

  • Hukumar asibitin koyarwa na jami'ar Abuja ta musanta labaran da ake yadawa kan mutuwar Obadiah Mailafia
  • Shugaban asibitin, Farfesa Ekele, ya ce cutar korona ce ta kashe Mailafia kuma ta tsananta kafin a kai shi cibiyar killacewansu
  • Ya kara da jaddada cewa basu taba cewa sai an basu kudi ba kafin su karba mara lafiya ko kuma fara duba shi

UATH, Abuja - Hukumomin asibitin koyarwa na jami'ar Abuja sun kwatanta labaran da ake yadawa kan abinda ya yi sanadin mutuwar tsohon mataimakin shugaban babban bankin Najeriya, Obadiah Mailafia da tsabar karya.

Hukumar asibitin ta tabbatar wa da Premium Times a ranar Litinin da yammaci cewa, Mailafia ya rasu ne sakamakon cutar korona da yayi fama da ita.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari za ta san matsayar bashin $4bn nan da kwana 7, kwamiti zai zauna

Bincike: Yadda tsohon mataimakin gwamnan CBN, Mailafia ya rasu, Jami'ai
Bincike: Yadda tsohon mataimakin gwamnan CBN, Mailafia ya rasu, Jami'ai. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Bayanin da hukumar asibitin ya zo ne da sakamakon dokar aiki da ke bukatar tsananin sirri kan marasa lafiya.

Kamar yadda shugaban asibitin, Farfesa Bissallah Ekele,ya ce tun kafin nan, wasu asibitoci biyu sun karba Mailafia inda aka tabbatar da cewa ya na dauke da cutar korona kafin a tura shi asibitin jami'ar koyarwa na Abuja domin killace shi lokacin da jikin shi ya tsananta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zargi

A ranar Lahadi, 'yan Najeriya sun samu mummunan labarin mutuwar tsohon masani a fanni kudi kuma tsohon dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) a zaben 2019.

Matsayar Mailafia kan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari na iya zama dalilin da yasa jama'a suka nuna damuwarsu tare da zargin musabbabin mutuwarsa.

Wata kungiya a yankin tsakiya na kasar nan a ranar Litinin, ta fitar da takarda inda ta zargi hukumar asibitin kan yadda marigayin mai shekaru 64 ya rasa ransa.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Atiku ya samu karbuwa a jam'iyyun siyasa 17 na kudanci

A martaninsa, Ekele ya kwatanta dukkan zargin da aka yi wa asibitin da karya tare da abun mamaki.

Ya ce:

"A matsayina zan iya tabbatar muka da cewa labaran bogi ne ke yawo a kafafen sada zumunta. Ba mu taba bukatar wasu kudi tun farko daga mara lafiya ba kafin mu fara duba shi. Likitan da ke aiki a ranar ya karba marasa lafiya kuma bai taba hana sanya wa mara lafiya na'urar taimakon numfashi ba."

Ekele ya ce marigayi Mailafia ya zo da cutar korona mai tsanani kuma tun kafin a kawo shi asibitin lamarin ya tsananta, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Nan da shekaru 2 za a kammala wurin kiwon shanun jihar Kaduna na N10bn, El-Rufai

A wani labari na daban, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna a ranar Talata, ya ce jiharsa ta fara aikin naira biliyan goma na gina wurin kiwo ga makiyaya a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Rai bakon duniya: Babban alkalin kotun daukaka kara na Kano ya kwanta dama

Daily Trust ta ruwaito cewa, El-Rufai, wanda ya zanta da manema labarai yayin wani taro da jami'an jam'iyyar APC a sakateriya jam'iyyyar da ke Abuja, ya ce nan da shekaru biyu za a kammala aikin.

Gwamnan ya ce babban bankin Najeriya na CBN shi ya taimaka wa jihar da kudi har N7.5 biliyan domin samun nasarar aikin, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel