Borno: An kama 'boka' da ya amshe N16m hannun wani da sunan zai masa asirin kuɗi

Borno: An kama 'boka' da ya amshe N16m hannun wani da sunan zai masa asirin kuɗi

  • EFCC ta kama wani boka da abokin aikinsa da suka damfari wani mutum kudi N16m a Borno
  • Bincike ya nuna cewa an bawa mutumin N22.2m ne ya yi sana'ar kiwon shanu amma ya kai wa boka N16m don ya yi masa asirin kuɗi
  • Bayan amshe N16m, bokan ya bashi wasu ƴan kayayyaki ya kuma umurci ya yi azumin wata 3 da kwana ɗaya

Jihar Borno - Jami'an hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC a Maiduguri sun kama wani 'boka' Mohammed Ibrahim da abokin aikinsa Ibrahim Abubakar kan damfarar wani Mohammed Gaji kuɗi N16m.

The Punch ta ruwaito cewa Mohammed da Abubakar sun damfari Gaji ne da sunan za su yi masa 'adduar' yin kuɗi.

Borno: An kama 'boka' kan karɓar N16m hannun wani da sunan zai masa asirin kuɗi
Jami'an hukumar EFCC. Hoto: The Punch
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kakakin Jam'iyyar APC Mai Mulki Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa

An kama su ne a Sabon Balori bayan Chad Basin a jihar Borno kamar yadda rahoton na The Punch ya bayyana.

Kakakin EFCC, Wilson Uwajaren, cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce an shigar da ƙara kan Gaji ana zargin ya ɓannatar da N22.2m da Mohammed Bukar ya bashi domin kafa wurin kiwon shanu na zamani.

Yadda lamarin ya faru?

Sanarwar ta kara da cewa:

"A maimakon ya yi amfani da kuɗin kamar yadda aka shirya da shi, Gaji ya ce ya bawa Mohammed N16m cikin N22.2m domin a yi masa addu'o'in yin kuɗi."

Bayan kama Gaji, ya amsa ya ɓannatar da kuɗin amma ya ce ya bawa wani 'malami' N16m ya kuma masa alkawarin zai azurta shi.

Uwajaren ya ce yayin samame an gano wani babban rami da aka rufe da fatar dabba a tsakiyar teburi a ɗaki inda wanda ke haɗa baki da Mohammed, wato Abubakar ke ɓoye wa, yana ƙaryar wai shi aljanni ne.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Zata Sha Ƙasa a Zaɓen 2023 Matukar Ta Tsayar da Ɗan Arewa, Jigon PDP

Sanarwar ta cigaba da cewa:

"Gaji ya yi ikirarin an bashi wani dutse mai daraja, da karamin akwai dauke da farin ƙyalle a ciki aka umurci ya yi azumi na wata uku da kwana ɗaya kafin ya yi kudin."

Sauran kayayyakin da aka gano sun hada da fararen ƙyalle da rubutun harshen larabci, ƙwarya, fatar dabbobi, ƙahon dabbobi, kudaden kasar waje da ƙananan akwati na ƙarfe.

'Yan sanda sun damke ma'aikacin banki da ya kwashewa kwastoma N10m daga asusunsa

A wani labarin daban, Hukumar ‘yan sandan jihar Oyo sun kama wani Adeyemi Tosin, mai shekaru 36, wanda ma’aikacin banki ne bisa zarginsa da kwasar naira miliyan 10 daga asusun wani abokin huldar bankin, Oladele Adida Quadri.

Kakakin hukumar, DSP Adewale Osifeso, ya bayyana hakan a wata takarda a ranar Talata, 17 ga watan Augusta, inda yace Tosin ya saci kudin Quadri, mai shekaru 78 ne da sunan zai taimake shi a reshen bankin na Ibadan bisa matsalar da ya samu wurin cirar kudi a ranar 12 zuwa ranar 13 ga watan Augusta.

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen dan majalisar arewa ya bayyana dalilin da ya sa APC ke zawarcin Jonathan, ya yi magana akan kudirin Tinubu

Binciken ‘yan sandan ya haifi da mai ido sakamakon umarnin kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ngozi Onadeko, wacce tasa a yi bincike na musamman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel