Gwamnan Kano Ganduje ya yi magana a game da wanda zai gaji kujerarsa a 2023

Gwamnan Kano Ganduje ya yi magana a game da wanda zai gaji kujerarsa a 2023

  • Abdullahi Umar Ganduje ya tabo batun siyasar jihar Kano a zabe mai zuwa
  • Gwamnan ya bayyana cewa bai da wani ‘dan takara a ransa a halin yanzu
  • Gwamna Ganduje yace duk masu neman takarar 2023 a APC sun cancanta

Kano - Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi hira da gidan talabijin Trust TV, inda ya tabo batutuwa da-dama daga rayuwarsa, siyasar APC zuwa mulki.

Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi magana game da rade-radin da ake yi na cewa yana da ‘dan takara a ransa wanda yake sa rai shi zai gaji kujerarsa a 2023.

Daily Trust ta rahoto Abdullahi Umar Ganduje yana cewa babu wanda yake da shi a rai a zaben 2023, yace jagorancin Kanawa ne a aikin da ke gabansa yanzu.

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen dan majalisar arewa ya bayyana dalilin da ya sa APC ke zawarcin Jonathan, ya yi magana akan kudirin Tinubu

Mulkin jama'a ke gaba na ba siyasa ba - Ganduje

“Akwai sauran lokaci sosai kafin zaben 2023, kuma abin da kuke karanta wa a jaridu ba gaskiya ba ne. Karya ce, kuma mutanen Kano sun sani.”
“Ban da wani ‘dan takarar Gwamna ko Sanata ko wata kujerar siyasa. Mun fi damu wa da jagorancin jama’a har lokacin shirya zabe ya yi.”

Gwamnan Kano Ganduje
Gwamna Abdullahi Ganduje Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ya za a fito da 'yan takara a Kano?

Gwamna Abdullahi Ganduje yace duk masu harin wata kujera a karkashin jam’iyyar APC sun cancanta, yace idan lokacin ya yi za a zauna a ga abin da za a yi.

Ganduje wanda ya fara siyasa tun a 1978 yace idan ta kama za a iya yin sulhu tsakanin ‘yan takara.

Kara karanta wannan

Takarar mataimakin shugaban kasa ko sanata: Makomar Ganduje bayan sauka a kujerar gwamna

“Ina tabbatar maka da cewa muna nan a dunkule. Duk wasu masu sha’awar neman takara a iya tunaninmu, ‘yan siyasan kwarai ne, za su iya takara.”
“Idan lokacin ya zo, hakkinmu ne mu zauna a tsakaninmu, idan ta kama ayi sulhu wajen takarar kamar yadda tsarin APC da dokar kasa ta tanada.”

Gwamnan ya bayyana cewa ya rike mukamin shugaban karamar hukuma sau uku a Abuja, sannan ya yi Kwamishina kafin ya shiga gidan gwamnati a 1999.

Ina labarin Murtala Garo?

Kwanakin baya Mai dakin gwamnan Kano, Hafsat Ganduje ta nuna Surukin Kwankwaso, Murtala Sule, tace irinsu ne ya kamata su yi mulki jihar Kano a zabe mai zuwa.

A karshe dole Gwamnatin Jihar Kano ta bakin kwamishinan labarai, Muhammad Garba ta musanya rade-radin cewa Murtala Garo ne zai gaji Abdullahi Ganduje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel