Tashin hankali yayin da ‘yan bindiga suka kashe mutum biyu a Anambra

Tashin hankali yayin da ‘yan bindiga suka kashe mutum biyu a Anambra

  • 'Yan bindiga sun halaka wasu mutane biyu da ke tafiya kan hanya a jihar Anambra
  • Lamarin ya afku ne da misalin karfe 12:30 na ranar Talata, 21 ga watan Satumba, a yankin unguwar Udoka da ke Awka, a kan babbar hanyar Onitsha zuwa Enugu
  • Kakakin rundunar ‘yan sandan Anambra, Ikenga Tochukwu, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce lamarin ya shafi kungiyoyin asiri ne

Anambra - Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe wasu mutane biyu da ba a san ko su waye ba a jihar Anambra.

Lamarin, wanda ya wakana da misalin karfe 12:30 na ranar Talata, 21 ga watan Satumba, ya faru ne a yankin unguwar Udoka da ke Awka, a kan babbar hanyar Onitsha zuwa Enugu.

Tashin hankali yayin da ‘yan bindiga suka kashe mutum biyu a Anambra
Tashin hankali yayin da ‘yan bindiga suka kashe mutum biyu a Anambra Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Wasu da abun ya faru a kan idonsu sun ce wadanda abin ya rutsa da su yan kasuwa ne.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare motar 'yan sanda sun kashe jami'ai, sun bakawa motarsu wuta

Wani wanda abin ya faru a idonsa, wanda ya zanta da jaridar The Nation, ya yi ikirarin cewa yan bindigan kashe su ne ta hanyar harbin su ba tare da sun kwace komai daga gare su ba.

Majiyar ta ce:

“Na gan su. Kawai sun harbe mutanen biyu wadanda suka kasance yan kasuwa a yankin sannan suka tafi.
“Babu abin da aka kwace daga gare su. Ina zargin lamarin an aikesu su kashe su ne ko kuma abokan hamayyar kasuwanci ne."

Sai dai mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Anambra, Ikenga Tochukwu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce lamarin ya shafi kungiyoyin asiri na hamayya ne.

Ya ce maharan sun tuko wata mota kirar Mercedes 190 sannan suka harbe mutanen wadanda ke tafiya akan titi da misalin karfe 12.30 na rana sannan suka yi gaba abinsu.

Kara karanta wannan

Makashin Ɗan Sanata Na'Allah: Buhunan Shinkafa 23 Na Siya Da Kason Kuɗi Na

Tochukwu ya ce:

“Binciken farko ya nuna lamarin yaki ne na kungiyoyin asiri. Kwamishinan ‘yan sanda, Tony Olofu, ya ba da umarnin a gudanar da bincike kan lamarin.”

Ya ce an kwashe gawarwakin wadanda abin ya rutsa da su daga wurin da aka aikata laifin kuma an ajiye su a dakin ajiye gawarwaki, Nigerian Tribune ta ruwaito.

'Yan bindiga sun tare motar 'yan sanda sun kashe jami'ai, sun bakawa motarsu wuta

A wani labarin, mun kawo a baya cewa akalla ‘yan sanda uku aka kashe a garin Onitsha, jihar Anambra sakamakon harin 'yan bindiga.

Lamarin ya faru ne a hanyar Ukaegbu/Ezeiweka a Onitsha a safiyar Lahadi 19 ga watan Satumba, 2021.

An kuma kona wata motar sintiri kurmus ta jami'an da suka mutu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng