Makashin Ɗan Sanata Na'Allah: Buhunan Shinkafa 23 Na Siya Da Kason Kuɗi Na

Makashin Ɗan Sanata Na'Allah: Buhunan Shinkafa 23 Na Siya Da Kason Kuɗi Na

  • Daya daga cikin wadanda suka kashe dan Sanata Na'Allah ya ce shinkafa ya siya da kasonsa na kudin
  • Wanda ake zargin, Nasiru Salisu, ya ce buhunan shinkafa 23 ya siyo amma jami'an kwastam suka kama shinkafar
  • Salisu ya ce sun tafi gidan mamacin ne da niyyar su sace motarsa amma ya yi dambe da su hakan ya yi sanadin mutuwarsa

Jihar Kaduna - Daya daga cikin wadanda ake zargi da hannu wurin kashe Abdulkareem Na'Allah, dan Sanata Bala Ibn Na'Allah, ya ce ya yi amfani da kudin ne ya siya buhunan shinkafa, rahoton Daily Trust.

Ya bayyana hakan ne yayin da 'yan sanda suka yi holensa a ranar Alhamis a Kaduna kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Makashin Ɗan Sanata Na'Allah: Buhunan Shinkafa 23 Na Siya Da Kason Kuɗi Na
Wadanda ake zargi da kashe dan Sanata Na'Allah. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Bawa: Abinda ya faru da ni bayan an gaggauta fitar da ni daga Aso Rock

Nasiru Salisu, mai shekaru 27 a duniya, daya daga cikin wadanda ake zargin ya ce Bashir Muhammad, babban wanda ake zargin ne ya kitsa masa su aikata laifin.

Ya ce:

"Buhunnan shinkafa 23 na siya da kason kudin nawa da na samu amma jami'an hukumar hana faskwabri (kwastam) suka kama kayan."

Muhammad ya ce niyyarsu kawai shine su sace motar marigayin amma ya yi dambe da su hakan kuma ya yi sanadin rasuwarsa.

Mutuwar Abdulkareem Na'aAllah

A ranar 29 ga watan Augustan 2021 aka gano gawar Abdulkareem, babban dan sanatan a dakin sa da ke Malali GRA a Kaduna.

Sai dai babu kwararan bayanai a kan wadanda aka kama amma dai shekarun su 20 da ‘yan kai da haihuwa.

An tsinci abin hawan mamacin a wuraren iyakar Nijar.

Daily Trust ta tabbatar da kamen har ta tuntubi Kakakin rundunar ‘yan sandan yankin, ASP Jalige Mohammed ya ce:

Kara karanta wannan

Dalilin da Yasa Muka Kashe Ɗan Sanatan APC a Kaduna, Matasan da Aka Cafke Sun Yi Bayani

“Tabbas akwai wasu mutane 2 da ake zargin su ne makasan Abdulkareem Na’Allah,”

Mahaifin mamacin shine ke wakiltar mazabar Kebbi ta kudu a majalisar dattijai.

Wani mutum ya gamu da ajalinsa yayin da ya shiga maƙabartar musulmi cikin dare don haƙo gawa

A wani labarin daban, wani mutum da ba a gano ko wanene ba ya mutu yayin da ya ke yunkurin hako gawa a makabarta da ke Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, Premium Times ta ruwaito.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a makabartar musulmi da ke Iberekodo, karamar hukumar Abeokuta ta Arewa na jihar Ogun.

Abimbola Oyeyemi, mai magana da yawun yan sandan jihar Ogun, ya tabbatarwa Premium Times afkuwar lamarin a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel