Zaben 2023: Gawuna, Maliya, Rurum da wasu jiga-jigan APC 10 da ke neman Gwamnan Kano
Tun a yanzu, siyasar Kano ta fara yin zafi inda ake faman fafutukar yakin shugabancin jam’iyyun PDP mai hamayya da APC mai mulki.
Haka zalika an fara hasashe kan wadanda ake ganin za su tsaya takarar kujerar gwamna a jam’iyyar APC bayan wa’adin Abdullahi Ganduje.
Jaridar Politicsdigest ta tattaro wasu daga cikin jiga-jigan APC da watakila su nemi tikitin gwamna, da kuma yadda za ta iya kaya wa da su.
1. Barau Jibrin
Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa, Barau Ibrahim Jibrin yana cikin wadanda ake ganin suna da goyon bayan Gwamna Abdullahi Ganduje.
Barau Jibrin ya na kan karonsa na biyu a majalisar dattawa a karkashin APC, ya taba zuwa majalisar wakilai, kuma ya yi kwamishina.
KU KARANTA: Sanata Kwankwaso ya ce zasu tura yara kusan 150 su samu Digiri
2. Nasiru Yusuf Gawuna
Tsohon shugaban karamar hukumar Nasarawa, Nasiru Yusuf Gawuna, yana tare da wasu manyan kusoshi a gwamnatin Dr. Abdullahi Ganduje.
Nasiru Gawuna shi ne mataimakin gwamnan jihar Kano tun 2018, kuma ya yi kwamishina a baya. Wasu na zarginsa da gazawa a gida a zaben 2019.
3. Inuwa Waya
Inuwa Waya ya na daga cikin wadanda ake ganin za su jarraba sa’arsu a 2023. Ana kishin-kishin cewa Waya zai ajiye aikinsa a NNPC, ya shiga siyasa.
Jaridar ta ce Waya lauya ne wanda ya rike darekta a bangaren shari’a na ma’aikatar mai na kasa watau NNPC, kafin a sauya masa wurin aiki kwanan nan.
4. Muazu Magaji
Muazu Magaji wanda aka fi sani da ‘Dan-Sarauniya ya na cikin masu sha’awar rike Kano. Ana yi wa tafiyar tsohon kwamishinan ayyukan take da Win Win.
Dansarauniya ya yi karatu a jami’o’in BUK da na Birtaniya, ya san kan aiki, amma kaifin-bakinsa ya jawo har ya rasa kujerarsa bayan rasuwar Abba Kyari.
5. Shaaban Ibrahim Sharada
Wani ‘dan siyasa mai tasowa da ake ganin zai nemi tikitin gwamnan jihar Kano a zaben 2023 shi ne ‘dan majalisar birni, Honarabul Shaaban Ibrahim Sharada.
Shaaban Ibrahim Sharada tsohon hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne wanda yanzu ake yabon rawar da yake taka wa a majalisar wakilan tarayya.
KU KARANTA: Zan yi maganin rashin tsaro idan na zama Shugaban kasa - Bello
6. Ismaeel Buba Ahmed
Har ila yau, wani tsohon hadimin shugaban kasa a jerin shi ne Ismaeel Buba Ahmed. Ana zargin matashin ‘dan siyasar ya na hangen kujerar gwamnan Kano.
Ismaeel Ahmed masanin shari’a ne wanda ya yi karatu a Abuja da kasar Amurka, ya taba lashe kujerar majalisa a CPC a 2011 kafin kotu ta ruguza zaben.
7. Muhuyi Magaji Rimingado
Shugaban hukumar Kano Public Complaints and Anti-Corruption Commission mai yaki da rashin gaskiya, Muhuyi Magaji Rimingado, zai iya neman takara a 2023.
Rimingado ya sha ban-bam da irinsu Hon. Ahmed da Shaaban Sharada, ya na tare da gwamnati. Kafin yanzu ya taba yin mataimakin shugaban karamar hukuma.
8. Kawu Sumaila
Honarabul Abdulrahman Kawu Sumaila ya taba neman tikitin gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar APC a 2014, amma bai iya kai ga samun nasara ba.
Kawu Sumaila tsohon ‘dan majalisar tarayya ne, kuma ya taba zama mai ba shugaban Najeriya shawara, a zaben 2019 ya nemi tikitin Sanatan Kano ta Kudu.
9. Kabiru Gaya
Tsohon gwamna Kabiru Ibrahim Gaya ya dade ya na hangen gidan gwamnatin jihar Kano. Babu mamaki Sanatan na kudancin Kano ya fito takara a zabe mai zuwa.
Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya dade a majalisar dattawa, ya ce ana kiran ya fito neman gwamna. Gaya ya taba yin gwamna na watanni a lokacin mulkin soja a 1992.
10. Kabiru Alhassan Rurum
Kabiru Alhassan Rurum wanda ya taba yin Kansila a Legas shi ne na karshe a jerinmu. Rurum gawurtaccen ‘dan siyasa ne da shi ma ya fito daga Kano ta Kudu.
Rt. Hon. Kabiru Rurum shi ne shugaban majalisar dokokin jihar Kano da ya ba gwamnati shawarar a tsige Muhammadu Sanusi daga sarautar Kano a 2020.
Asali: Legit.ng