Hotunan Damfareran Kwantena da ya murkushe mota a Jihar Legas

Hotunan Damfareran Kwantena da ya murkushe mota a Jihar Legas

  • Wata babban kwantena ta fado daga kan gada ta murkushe wata motar hawa a Legas
  • Hukumar agaji ta LASEMA na Legas ta ce an ceto dukkan mutane hudu da ke cikin motar
  • Lamarin ya faru ne a yammacin ranar Lahadi 19 ga watan Satumban shekarar 2021 a birnin na Legas

Jihar Legas - Wani Kwantena mai tsawon kara arba'in, a yammacin ranar Lahadi ya fadowa daga gadar Ojuelegba ya murkushe wata motar hawa, kamar yadda The Punch ta ruwaito.

A cewar hukumar bada agajin gaggawa na jihar Legas, LASEMA, mutane hudun da suka makalle a cikin motar duk an ceto su da ransu.

Hotunan Damfareren Kwatena da ya murkushe mota a Jihar Legas
Damfareren Kwatena da ya murkushe mota a Jihar Legas. Hoto: Lasema Response Unit
Asali: Facebook

LASEMA tace trelar ta samu matsala ne hakan yasa ta fado kan motar kirar Toyota Camry mai lamba KRD-822FX. Fasinjojin suna cikin motar har zuwa kimanin karfe 6.35 na yammacin ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Sanwo-Olu ya sa hannu kan dokar hana kiwo a fili a Legas

Shugaban LASEMA, Olufemi Oke-Osayintolu ya tabbatar da cewa mutane hudu ne suka makale a cikin motar kuma an ceto su kamar yadda Gazette NGR ta ruwaito.

Nosa Okunbor, mai magana da yawun LASEMA, ya ce mutane biyun da aka ceto (maza biyu da mata biyu) suna asibitin Marina ana ba su kulawa.

Da ya ke martani kan lamarin, Babban kwamandan FRSC na jihar Legas, Olusegun Ogungbemide ya gargadi masu manyan motocci da ba su kulawa da su su janye su daga titi ko kuma su fuskanci fushin hukuma.

Ya yabawa dukkan wadanda suka bada gudunmawa wurin ceto mutanen da ransu.

Ya shawarci masu ababen hawa su rika takatsantsan musamman yanzu da muke dosar kashen shekara.

A baya-bayan nan dai hatsari na yawn faruwa a gadar Ojuelegba.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga na luguden wuta a kudancin Kaduna

Ga hotunan a kasa:

Hoton Kwatena da ya murkushe mota kirar Toyota a Jihar Legas
Hoton Kwatena da ya murkushe mota a Jihar Legas. Lasema Response Unit
Asali: Facebook

Hotunan Damfarern Kwatena da ya murkushe mota a Jihar Legas
Ma'aikatan ceto yayin kokarin fito da mutanen da kwantena ta danne a Legas. Lasema Response Unit
Asali: Facebook

Hotunan Damfarern Kwatena da ya murkushe mota a Jihar Legas
Ma'aikatan Lasema yayin aikin ceto. Lasema Response Unit
Asali: Facebook

Hotunan Damfarern Kwatena da ya murkushe mota a Jihar Legas
Hotunan Damfarern Kwatena da ya murkushe mota a Jihar Legas. Lasema Response Unit
Asali: Facebook

Dan Nigeria ya mutu cikin barcinsa kwanaki 7 bayan samun kwangilar N69bn daga gwamnatin Amurka

A wani labarin, wani dan Nigeria, kwararre a bangaren fasahar kwamfuta, David Gbodi Odaibo ya mutu cikin barcinsa kwanaki bakwai bayan samun kwangilar $125 (kimanin Naira Biliyan 69) daga gwamnatin Amurka, LIB ta ruwaito.

Dan uwansa kuma shugaban kamfanin Retina-Al Health Incorporation, Mr Stephen Odaibo ne ya bayyana hakan a rubutun da ya yi a kafar LinkedIn.

Stephen yace dan uwansa bai kamu da cutar korona ba kuma ya yi rigakafi, amma ya samu bugun zuciya yayin da ya ke barci ya mutu yana da shekaru 42. Ya bayyana cewa rasuwar dan uwansa ya tada masa hankali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel