Dan Nigeria ya mutu cikin barcinsa kwanaki 7 bayan samun kwangilar N69bn daga gwamnatin Amurka

Dan Nigeria ya mutu cikin barcinsa kwanaki 7 bayan samun kwangilar N69bn daga gwamnatin Amurka

  • Allah ya karbi ran wani dan Nigeria mako daya bayan samun kwangilar N69bn a Amurka
  • Dan uwan mammacin ya bayyana cewa ya rasu ne cikin barcinsa sakamakon bugun zuciya
  • Cikin alhini, ya bayyana cewa dan uwansan ya rubuta manhaja ne da za a yi amfani da ita a filin tashin jiragen sama

Wani dan Nigeria, kwararre a bangaren fasahar kwamfuta, David Gbodi Odaibo ya mutu cikin barcinsa kwanaki bakwai bayan samun kwangilar $125 (kimanin Naira Biliyan 69) daga gwamnatin Amurka, LIB ta ruwaito.

Dan uwansa kuma shugaban kamfanin Retina-Al Health Incorporation, Mr Stephen Odaibo ne ya bayyana hakan a rubutun da ya yi a kafar LinkedIn.

Dan Nigeria ya mutu cikin barcinsa kwanaki 7 bayan samun kwangilar N69bn daga gwamnatin Amurka
David Gbodi Odaibo. Hoto: Mr Stephen Odaibo
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

IPOB: Gwamna Obiano ya bar gidan gwamnati, ya jagoranci zanga-zanga a kan titi

Stephen yace dan uwansa bai kamu da cutar korona ba kuma ya yi rigakafi, amma ya samu bugun zuciya yayin da ya ke barci ya mutu yana da shekaru 42. Ya bayyana cewa rasuwar dan uwansa ya tada masa hankali.

Kafin rasuwarsa, David ya rubuta wani manhaja da ke gano barazana a filayen tashin jiragen sama kuma ya gwamnatin Amurka ta bashi kwangilar $125 miliyan.

Wani sashi cikin abin da ya rubuta:

"Dan uwa na David Gbodi Odaibo, ya rasu jiya. Zuciya ta tana cike da alhini. Ya samu bugun zuciya ne a cikin barcinsa. Ya yi riga kafin korona kuma bai kamu da COVID 19 ba. Mun shaku sosai. Shekarunsu 42.
"a na da digirin digirgir a Kwamfuta Injiniya kuma ya zama 'Kaggle Master' kwarewa mafi girma a bangaren fasahar 'Machine Learning'.
"Ya rubuta manhajar gano barazanar hari a filayen tashin jiragen sama ya kuma samu kwangilar $125 daga sashi kula da tsaron gida na Amurka mako daya da ta gabata. Manhajar da ya rubuta ta fi na sauran kamfanonin da ke da biliyoyin naira. Nan gaba idan ka yi tafiya lafiya a jirgin sama, ka tuna da dan uwa na David."

Kara karanta wannan

Ba zan sake soyayya ba, cewar dan sadan da budurwa ta yaudara bayan ya kashe mata kudin makaranta

Gwamna ya haramtawa ma'aikata zuwa aiki har sai sunyi riga-kafin korona

A wani labarin daban, Gwamnatin Jihar Edo ta haramtawa ma'aikatan da ba su yi allurar riga-kafin korona ba shiga ofishosinsu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

The Cable ta ruwaito cewa gwamnatin ta hana dukkan wadanda ba su riga sun yi riga-kafin ba shiga wuraren taruwan mutane.

Tunda farko, Gwamna Godwin Obaseki, a cikin watan Satumba, ya hana wadanda ba a yi wa rigakafi shiga bankuna, ofisoshin gwamnati da wuraren ibada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel