Bayan barin gidan Sheikh Pantami, an ga Fani-Kayode ya je cin abinci a gidan wani Ministan

Bayan barin gidan Sheikh Pantami, an ga Fani-Kayode ya je cin abinci a gidan wani Ministan

  • Femi Fani-Kayode ya ziyarci George Akume bayan komawarsa jam’iyyar APC
  • Tsohon ‘dan adawan yace Ministan ne ya gayyace shi domin su ci abincin rana
  • Fani-Kayode yace ya tattauna mas’aloli da yadda za a gyara Najeriya da Akume

Abuja - Tun ranar Alhamis, 16 ga watan Satumba, 2021, ko ina ya cika da labarin Femi Fani-Kayode bayan gawurtaccen ‘dan adawar ya shiga jirgin APC.

Daily Trust tace masu sharhin siyasa suna sukar sauya-shekar da tsohon Ministan tarayyar ya yi.

Isa Ali Ibrahim Pantami ya zauna da FFK

A ranar Asabar, 18 ga watan Satumba, sai aka ga Femi Fani-Kayode a gidan Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani na kasa, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami.

Femi Fani-Kayode ya lashe amansa, ya zauna tare da mutumin da ya kira da sunaye iri-iri, har yana kira ga shugaban kasa ya tsige Ministan kwanakin baya.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa mambobin APC ke jin haushin shigowar Kayode jam'iyyarsu, DG PGF

Bayan ya bar gidan Isa Ali Pantami, sai kuma aka sake ganin hotunan tsohon jigon na jam’iyyar PDP tare da Ministan ayyuka na musamman a shafin Facebook.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Femi Fani Kayode
George Akume Femi Fani Kayode Hoto: www.nairaland.com
Asali: UGC

Jaridar tace Fani-Kayode ya wallafa hotunansa a gidan Sanata George Akume a birnin tarayya Abuja.

Da yake magana, Nairaland tace Fani-Kayode ya bayyana cewa Ministan ne ya gayyace shi domin su ci abicin dare, kamar dai yadda ya je gidan Isa Pantami.

Me ya kai FFK wajen Akume

“An karrama ni tare da daraja ni da aboki na, ‘danunuwa na, Sanata George Akume, tsohon gwamnan jihar Benuwai, Ministan ayyuka na musamman ya gayyace ni gidansa a Abuja.”
“Minista (George) Akume ya na cikin shugabannin da ake ganin girmansu kuma masu matukar hangen nesa a kasar nan. Abokantakar mu da shi ta zarce shekaru goma yanzu a Duniya.”

Kara karanta wannan

Jigon APC a Kano ya yi tir da tarbar da Buhari, APC suka yi wa Fani-Kayode a fadar Aso Villa

“Mun yi kus-kus bayan mun ci abincin rana, muka tattauna a kan muhimman batutuwan da suka shafi kasar nan, da yadda za a ciyar da Najeriya gaba. Na gode da tarbar da ya yi mani”

FFK ya shirga karya?

A makon da ya gabata ne Gwamnan Ebonyi ya yi wa Fani-Kayode kaca-kaca, yace ba shi ne ya jawo shi APC daga jam'iyyar PDP ba kamar yadda yake ikirari ba.

Dave Umahi yace Fani-Kayode bai san lokacin da ya fice daga jam’iyyar APC. Gwamnan ya yi kira ga 'dan siyasar ya janye wadannan kalamai da ya yi a makon jiya.

Hotunan zamansu a Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel