Satar waya ta N80,000: Ɗan kasuwa ya shigar da ƙarar karuwa a kotun shari'a a Kaduna

Satar waya ta N80,000: Ɗan kasuwa ya shigar da ƙarar karuwa a kotun shari'a a Kaduna

  • Wani Umar Aliyu, dan kasuwa, ya yi karar wata Fatima Aliyu a kotun shari'ar da ke Magajin Garin Kaduna
  • Aliyu ya yi karar Fatima ne kan zarginta da hadin baki da wasu maza biyu don sace masa wayarsa
  • Wadanda ake zargin sun musanta aikata laifin hakan yasa alkali ya dage cigaba da sauraron shariar

Wani dan kasuwa mai shekaru 30, Umar Aliyu, a ranar Juma'a ya yi karar wata Fatima Aliyu, karuwa a gaban alkalin kotun shari'a da ke Magajin Gari a Kaduna, kan zarginta da sace masa wayar salula da kudinta ya kai N80,000.

Mai shigar da karar, ya kuma yi karar wasu mutane biyu maza, Mohammad Tukur da Imran Tukur kan zarginsu da hadin baki da Fatima wurin aikata satar kamar yadda The Guardian ta ruwaito.

Satar waya ta N80,000: Ɗan kasuwa ya shigar da ƙarar karuwa a kotun shari'a a Kaduna
Wayar Salula ta zamani. Hoto: The Guardian
Asali: Facebook

The Guardian ta ruwaito Dan sanda mai gabatar da kara, Sufeta Ibrahim Shuaibu, ya shaidawa kotu cewa wanda ya yi karar ya yi ciniki da Fatima kuma ta amince masa kan N10,000.

Ya ce wanda ya shigar da karar ya tura kudin zuwa asusun bankin ajiya na Muhammad sannan daga bisani ya tsere da wayar.

Shuaibu ya ce hakan ya ci karo da sashi na 59, 142, da 271 na dokar Penal Code na jihar Kaduna.

Wadanda aka yi karar su sun musanta zargin da ake musu.

Wane mataki alkalin kotun ya dauka?

Alkalin kotun, Malam Murtala Nasir, ya bada belin wadanda ake zargin da sharadin za su gabatar da wadanda za su tsaya musu kuma su kasance amintattun mutane ne.

Mai shari'a Murtala Nasir ya dage cigaba da sauraron shari'ar har zuwa ranar 21 ga watan Satumban 2021 inda zai yanke hukunci.

Har cikin silin na ke ɓoye kuɗi amma tana shiga ta sace: Miji ya nemi a raba aure don satar da matarsa ke masa

A wani labarin daban, wata kotun gargajiya mai zamanta a Igando a jihar Legas, a ranar Alhamis ta tsinke auren mata da miji da suka shafe shekaru 10 suna zaman aure saboda halin sata da matar ke da shi, Premium Times ta ruwaito.

Mutiu Bamgbose, dan kasuwa mai shekaru 45, ya kuma zargi matarsa Aliyah da cin amanarsa na aure.

Da ya ke yanke hukunci, alkalin kotun, Adeniy Koledoye, ya ce babu tantama auren na su ba mai gyaruwa bane duba da cewa wacce aka yi karar ta ta ki amsa gayyatar kotun, Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel