Duk dan fanshon da ya zagi Kwankwaso sai ya shiga wuta, Kakakin Kwankwasiyya

Duk dan fanshon da ya zagi Kwankwaso sai ya shiga wuta, Kakakin Kwankwasiyya

  • Kakakin darikar Kwankwasiyya ya caccaki yan fanshin jihar Kano
  • Ya ce basu da godiyar Allah duk da abinda Rabiu Kwankwaso yayi musu
  • Yan fansho sun kai karar Kwankwaso ofishin hukumar EFCC

Kano - Dan takarar kujerar mataimakin gwamnan Kano a zaben 2019 karkashin jam'iyyar People Democratic Party (PDP), Aminu AbdulSalam, ya caccaki yan fanshon dake zagin maigidansa, Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.

Aminu AbdulSalam wanda shine Kakakin darikar Kwankwasiyya yace duk dan fanshon da ya zagi Kwankwado zai shiga wuta saboda marasa godiya ne.

Yace yan fanshon basu kyauta ba yayinda suka kai karar Kwankwaso wajen hukumar EFCC kan zargin yayi amfani da kudin fansho.

Aminu yayi magana a daren Alhamis a wani shirin gidan rediyon Express kan gayyatar da EFCC ta yiwa Kwankwaso kan zargin almundahana da karkatar da kudin al'umma da kuma baiwa abokansa gidaje, PremiumTimes ta jiyo

Kara karanta wannan

IGP Ga Jami'an Yan Sanda: Aikin Ku Zai Iya Jefa Ku Wuta Ko Aljanna Ranar Gobe Ƙiyama

Aminu AbdulSalam yace Kwankwaso ne ya karawa yan fansho kudi zuwa N5000 saboda haka duk dan fanshon da bai godewa hakan ba wuta zai shiga.

Duk dan fanshon da ya zagi Kwankwaso sai ya shiga wuta, Kakakin Kwankwasiyya
Duk dan fanshon da ya zagi Kwankwaso sai ya shiga wuta, Kakakin Kwankwasiyya Hoto: Rabiu Kwankwaso
Asali: Facebook

A cewarsa:

"Kwankwaso yayi iyakan kokarinsa wa yan fashi kuma duk dan fanshon da bai gode da abinda Kwankwaso yayi ba zai shiga wuta."

Za ku tuna cewa 2015, yan fanshi sun kai karar Kwankwaso wajen hukumar EFCC kan zargin karkatar da kudin fansho.

Kwankwaso ya yi kunnen uwar-shegu da gayyatar EFCC, akwai yiwuwar a yi ram da shi

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ki amsa gayyatar hukumar yaki da rashawa ta EFCC, a makon da ta gabata.

An gayyaci dan siyasan ne domin ya amsa tambayoyi da suka shafi zargin amfani da ofishinsa ba ta yadda ya dace ba, karkatar da kudaden al'umma da bawa wasu na kusa da shi gidaje ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace wani limamin Katolika, sun kashe mutane 11 a jihar Kaduna

Majiyoyi sun ce an bukaci Kwankwaso, jigo a jam'iyyar PDP ya bayyana a hedkwatar EFCC a ranar Alhamis da ta gabata a Abuja amma ya ki amsa gayyatar.

Kwankwaso bai amsa sakon kar ta kwana ba da aka aika masa domin jin ta bakinsa game da lamarin. Bai kuma daga wayarsa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel