Yadda Waɗanda Suka Kashe Ɗan Sanatan APC Suka Karya Darajar Motarsa Ta N9m Suka Sayar N1m

Yadda Waɗanda Suka Kashe Ɗan Sanatan APC Suka Karya Darajar Motarsa Ta N9m Suka Sayar N1m

  • Mutane 2 da ake zargin sun halaka Abdulkareem Ibn Na’Allah sun bayyana cewa sun sayar da motar sa da suka sata N1m a Katsina
  • Wadanda ake zargin sun bayyana wa manema labarai hakan a ranar Alhamis yayin da aka kai su hedkwatar rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna
  • Kakakin rundunar ‘yan sandan yankin, ASP Muhammad Jalige ya sanar da manema labarai cewa kimar motar ta kai N9m

Jihar Kaduna - Mutane biyu da ake zargin sun halaka Abdulkareem Ibn Na’Allah, babban dan sanata Bala Ibn Na’Allah, sun ce sun sayar da motar sa naira miliyan 1, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Wadanda ake zargin, Bashir Muhammad mai shekaru 23 da Nasiru Balarabe mai shekaru 27 sun bayyana wa manema labarai hakan a ranar Alhamis yayin da aka kai su ofishin rundunar ‘yan sanda da ke Kaduna.

Kara karanta wannan

Sojoji Sun Cafke Sajan Ɗan Sanda Da Harsasai 370 a Plateau

Yadda Waɗanda Suka Kashe Ɗan Sanatan APC Suka Karya Darajar Motarsa Ta N9m Suka Sayar N1m
Matasan da ake zargi sun kashe dan Sanata Na'Allah. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kimar motar ya kai N9m

Kakakin rundunar, ASP Muhammad Jalige ya sanar da manema labarai cewa motar Abdulkareem ta kai kimar naira miliyan 9.

Yayin amsa tambayoyin manema labarai, daya daga cikin wadanda ake zargin, Balarabe, mazaunin Kawo ne a jihar Kaduna, ya ce sun sayar da motar a naira miliyan 1 a Katsina.

Balarabe ya yi amfani da kudin sa wurin siyan shinkafar kasar waje, amma jami’an hukumar fasa kwauri sun kama shi a iyakar kasa sannan su ka kwace shinkafar.

Daily Nigerian ta ruwaito ya ce:

“Na siya buhunan shinkafa 23 da nawa kudin amma jami’an fasa kwauri sun kwace."

Dayan matashin ya ce ba talauci bane ya sa shi aikata ta’addancin

Dayan, Muhammad, mazaunin layin Rabah dake Kaduna ya ce bai san mamacin ba sai ranar da su ka halaka shi.

Kara karanta wannan

Rundunar sojin saman Najeriya ta fara bincike kan barin wuta da jirgin yaki ya yi kan fararen hula a Yobe

Da aka tambayi Muhammad idan talauci ne ya sa ya aikata wannan laifin, ya ce iyayen sa suna iyaka kokarin su wurin wadata shi.

Sai dai Kakakin rundunar ‘yan sanda, Jalige ya ce a jamhuriyar Nijar suka sayar da motar, an dawo da ita Najeriya ne bayan sun daidaita da jami’an da ke tsaron iyakar kasa da kasa.

Makashin Ɗan Sanata Na'Allah: Buhunan Shinkafa 23 Na Siya Da Kason Kuɗi Na

A wani labarin mai alaka da wannan, Daya daga cikin wadanda ake zargi da hannu wurin kashe Abdulkareem Na'Allah, dan Sanata Bala Ibn Na'Allah, ya ce ya yi amfani da kudin ne ya siya buhunan shinkafa, rahoton Daily Trust.

Ya bayyana hakan ne yayin da 'yan sanda suka yi holensa a ranar Alhamis a Kaduna kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Nasiru Salisu, mai shekaru 27 a duniya, daya daga cikin wadanda ake zargin ya ce Bashir Muhammad, babban wanda ake zargin ne ya kitsa masa su aikata laifin.

Kara karanta wannan

An Cafke Hatsabibin Ɓarawon Shanu Da Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi a Jihar Katsina

Asali: Legit.ng

Online view pixel