Jerin ayyukan da za ayi da sabon bashin tiriliyoyin kudin da Shugaba Buhari yake so ya karbo

Jerin ayyukan da za ayi da sabon bashin tiriliyoyin kudin da Shugaba Buhari yake so ya karbo

  • Gwamnatin Tarayya tana neman a bata dama ta karbo $4.9bn daga kasar waje
  • Jihohin Kano, Legas Taraba, Nasarawa, da Kogi za su amfana idan aka ci bashin
  • Za a narka wani kaso daga cikin kudin a aikin jirgin kasan Maradi da na Ibadan

Abuja - Titin dogon jirgin kasan Kano zuwa garin Maradi a kasar Nijar yana cikin ayyukan da ake sa rai za ayi da sabon bashin da gwamnati take nema.

Jaridar Punch ta rahoto shugaban kasa yana so majalisa ta amince masa ya karbo bashi domin a aiwatar da wasu ayyuka a cikin tsare-tsaren 2018-2020.

A wasikar da shugaban kasa ya aika wa ‘yan majalisa a baya, ya bayyana cewa za a yi wa kowane yankin kasar nan ayyuka da makudan kudin da za a aro.

Kara karanta wannan

An saki bidiyo yayin da kwamandan IPOB/ESN Shakiti-Bobo ya ambaci sunan mai daukar nauyin kungiyoyin

Dogon Kano-Katsina-Daura-Jibiya-Maradi

Majiyar jaridar ta bayyana cewa da wannan tulin bashi ne za a soma aikin titin jirgin kasan Kano-Maradi, wanda za a tsaya a garin Dutse, jihar Jigawa.

Shugaba Muhammadu Buhari yace jirgin kasan da zai hada Kano-Katsina-Daura-Jibiya-Maradi zai bunkasa kasuwancin Najeriya da Arewacin Afrika.

Jirgin kasa
Jirgin kasan Legas zuwa Ibadan Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Legas za ta ci moriyar bashin

Idan an karbo aron kudin ne za ayi amfani da fam $225,120,000 daga bankin China Exim Bank domin a kammala titin jirgin kasan Legas zuwa Ibadan.

A yankin Kudu maso yamma, za ayi aiki a tashoshin ruwan Apapa da Tincan da wannan bashin.

Sauran jihohin da za su ci moriyar bashin kudin sun hada da; Anambra, Benuwai, Ebonyi, Neja, Ogun. Sai kuma jihohin Taraba, Nasarawa, Enugu da jihar Kogi.

Kara karanta wannan

Wani kamfani zai biya makudan kudade ga mai son ya kalli wasu fina-finai 13

Ana sa rai kudin da za a karbo ya kai ga manoma 100, 000 da masu gyaran kayan hatsi 3, 000. Har ila yau ‘yan kasuwa 6, 000 aka yi kasafi za su amfana da bashin.

Rahoton yace Bankin Sin zai taimaka da $276,981,587 daga cikin kudin, wanda za ayi amfani da shi wajen bunkasa harkar wutar lantarki a wasu wurare a kasar.

Najeriya na da bashin N33tr

Dazu kun ji cewa Gwamnonin jihohi 36 da birnin tarayya Abuja ke da kusan Naira tiriliyan 6 a cikin bashin Naira tiriliyan 33 da gwamnatin Najeriya ta ci bashi.

DMO tace Indiya na cikin kasashe 5 da Najeriya ta fi yawan rugawa wajen su neman aron kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel