Ya zama dole a baiwa Kudancin Najeriya kujerar shugaban kasa a 2023

Ya zama dole a baiwa Kudancin Najeriya kujerar shugaban kasa a 2023

  • Gwamnonin Kudancin Najeriya sun ce a 2023, mulki wajibi ne ya dawo hannusu
  • Gwamnonin sun gana a Enugu inda suka ittifaki kan wasu abubuwa
  • Gwamnonin sun jaddada niyyar haramta kiwo a fili gaba daya a yankin

Enugu - Kungiyar gwamnonin kudancin Najeriya ta bayyana cewa ya zama wajibi shugaban kasan Najeriya na gaba a 2023 ya kasance daga yankin.

Kungiyar karkashin shugaban gwamnonin kuma gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, sun gana ne ranar Alhamis a jihar Enugu, Kudu maso gabashin Najeriya.

A ganawar, gwamnonin sun jaddada matsayarsu na baya na hana kiwo a fili da kuma shigar da wasu sauye-sauye cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Akeredolu wanda ya bayyana abubuwan da suka yanke a jawabi bayan taron, yace gaba daya gwamnonin sun yi ittifaki kan cewa wajibi ne shugaban ƙasa na gaba a Najeriya ya fito daga Kudu

Kara karanta wannan

An saki bidiyo yayin da kwamandan IPOB/ESN Shakiti-Bobo ya ambaci sunan mai daukar nauyin kungiyoyin

Akeredolu ya ce

"Dukkanmu gwamnonin yankin mun yi ittifaki wajibi ne shugaban ƙasa na gaba ya fito daga Kudu. Duk da cewa har yanzu ba mu tsayar da mutum ɗaya da zai fito takaran zaben 2023 ba."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya zama dole a baiwa Kudancin Najeriya kujerar shugaban kasa a 2023
Ya zama dole a baiwa Kudancin Najeriya kujerar shugaban kasa a 2023 Hoto: Southern Governors Forum
Asali: Facebook

Gwamnonin dake hallare a ganawar sune gwamnan Enugu Ifeanyi Ugwuanyi; Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas; Rotimi Akeredolu na jihar Ondo; Nyesom Wike na jihar Rivers; Adegboyega Oyetola na Osun; Ifeanyi Okowa na Delta, da kuma Doye Diri na Bayelsa.

Sauran gwamnonin sune gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, da na Akwa Ibom, Emmanuel Udom.

Mataimakan gwamnan da suka wakilci gwamnoninsu sune Otunba Bisi Egbeyemi na Ekiti; Rauf Olaniyan na jihar Oyo; Prof Evara Esu na Cross River; Ude Okochukwu na Abia, Kelechi Igwe na Ebonyi; Philip Shaibu na Edo; da Placid Njoku na Imo.

Kara karanta wannan

2023: Arewa za ta tashi da tikitin shugaban kasa a PDP, Yarbawa da Shugaban Jam'iyya

Asali: Legit.ng

Online view pixel