‘Yan Majalisar Jihar Kano sun yarda Gwamna Ganduje ya karbo bashin Naira Biliyan 4

‘Yan Majalisar Jihar Kano sun yarda Gwamna Ganduje ya karbo bashin Naira Biliyan 4

  • ‘Yan Majalisar dokokin jihar Kano sun amince da rokon karbo aron kudi
  • Gwamna Abdullahi Umar Ganduje zai ci sabon bashin Naira biliyan hudu
  • Za ayi amfani da bashin domin kammala aikin wuta a Tiga da Challawa

Kano - Majalisar dokokin jihar Kano ta karbi rokon gwamnati na neman bashi. Jaridar Punch tace ‘yan majalisar jihar sun amince da wannan bukata.

Rahoton yace majalisar jihar Kano ta yarda gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya karbo bashin Naira biliyan hudu domin a inganta wutar lantarki.

Majalisar ta amince da wannan roko a ranar Laraba, 15 ga watan Satumba, 2021, bayan shugaban majalisa ya karanto wasikar Dr. Abdullahi Ganduje.

Hamisu Chidari ya karanto bukatar Ganduje

Shugaban majalisar dokoki na jiha Kano, Rt. Hon. Hamisu Chidari ya karanta wasikar domin a tattauna a kanta a zauren majalisar a ranar Larabar.

Kara karanta wannan

Bayan Ta Yi Fatali da Gayyatar EFCC, Matar Ganduje Ta Shilla Landan Wurin Bikin Kammala Karatun Ɗanta

Da aka gabatar da wasikar, shugaban masu rinjaye, Hon. Labaran Madari, ya nemi abokan aikinsa su amince a ba gwamna damar karbo wannan bashi.

Labaran Madari yace idan gwamnati ta karbo aron kudin, mutanen Kano za su amfana sosai. A karshe ‘yan majalisar sun yi na’am da wannan batun.

Gwamnan Jihar Kano
Gwamna Abdullahi Ganduje Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Me za ayi da kudin?

Za ayi amfani da wannan kudi ne domin ayi aikin wuta a datsen ruwan Tiga da kuma Challawa.

Freedom Radio tace Gwamna Ganduje yace za a batar da kudin domin a kammala aikin samar da hasken wutar lantarki daga ruwan Tiga da na Challawa.

Idan an dace, za ayi amfani da wutan wajen haska asibitoci, fitilun kan hanya da gidajen ruwa.

A zaman da aka yi, ‘yan majalisar Karaye da Albasu, Nasiru Dutsen Amare da Sunusi Bataiya sun bukaci gwamnati ta samar da makabatu a yankunansu.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Hotuna sun bayyana yayin da Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinonin INEC

Kafin a tashi, sauran ‘yan majalisar na jihar Kano sun yi na’am da wannan kudirin da aka kawo.

Buhari zai sake cin bashi?

Duk da ana bin Najeriya bashin N33tr, kun ji cewa Muhammadu Buhari yana neman majalisar dattawa ta sake ba shi damar ya karbo bashin wasu N2tr.

Jam’iyyar APC tace ana cin bashi ne domin ayi ayyuka ba a wawuri kudi kamar yadda PDP ta yi ba. APC tace har yanzu ana biyan wani bashin da PDP ta ci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel