Da yan IPOB, da yan Oduduwa, duk yan ta'adda ne kamar Boko Haram: Kakakin Majalisa

Da yan IPOB, da yan Oduduwa, duk yan ta'adda ne kamar Boko Haram: Kakakin Majalisa

  • Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa idan ba'a dau mataki ba, wata sabuwar fitina na hanyar bullowa
  • Kaakin majalisa ya bayyana masu rajin kafa kasar Biafra da Oduduwa matsayin yan ta'adda
  • Yan Oduduwa sun gudanar da zanga-zanga a majalisar dinkin duniya

Abuja - Kakakin Majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa abinda masu rajin ballewa daga Najeriya ke yi kwanakin nan ya nuna cewa basu da banbancin da yan ta'addan Boko Haram.

Ya bayyana hakan ranar Laraba a jawabin maraba da mambobin majalisar bayan makonni tara suna hutu, rahoton PremiumTimes.

A ranar 15 ga Yuli, yan majalisar sun tafi hutun shekara.

Femi Gbajabiamila yace nan da lokaci kadan, wadannan masu son ballewa daga Naeriya zasu kai Najeriya zuwa ga halaka.

Kara karanta wannan

Yadda Yan bindiga suka yi awon gaba da Sarkin Bungudu a titin Kaduna/Abuja

A cewarsa, sun fara zama matsala ga tsaron Najeriya.

Yace:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ya zama wajibi mu fara kallon wannan lamari matsayin sabon barazana saboda hadari. A Kudancin Najeriya, Gabas da yamma, wasu malalata kuma yan iska suna lullubi da sunan masu rajin ballewa daga Najeriya domin kawo matsala, kashe mutane da kuma kawo cikas ga tattalin arzikin sauran yan Najeriya."
"Wadannan mutane, bisa takurawa jama'a da sukayi, lalata dukiyoyin mutane, hana dalibai zuwa makaranta, hana yan kasuwa fita, kin son zama don sulhu da kuma jin ra'ayin wani, ya nuna cewa basu da banbancin da yan Boko Haram da ISWAP."
"Nan da lokaci kadan, zasu kai wannan kasar tamu ga halaka."

Da yan IPOB, da yan Oduduwa, duk yan ta'adda ne kamar Boko Haram: Kakakin Majalisa
Da yan IPOB, da yan Oduduwa, duk yan ta'adda ne kamar Boko Haram: Kakakin Majalisa

Orji Kalu ga FG: Ku yafe wa magoya bayan Igboho da ke hannun ku kamar yadda kuka yafe wa ƴan Boko Haram

Kara karanta wannan

Ku taimakawa Almajirai wajen samun ilmin Boko: Rochas Okorocha

Mai tsawatarwa a majalisar dattawa, Sanata Orji Kalu ya bukaci gwamnatin tarayya ta yafe wa masu rajin kafa kasar Yarabawa, IPOB da ke hannun jami’an tsaro.

Tsohon gwamnan Jihar Abia ya ce ya kamata a yafe musu kamar yadda aka yafe wa tubabbun ‘yan Boko Haram da sauran ‘yan bindiga.

A wata takarda ta ranar Talata, 14 ga watan Satumba, Kalu ya ce yafe musu zai kawo hadin kai da zaman lafiya a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng