AIB ya gabatar da abubuwa 27 da aka gano a binciken mutuwar Janar Attahiru a jirgin sama

AIB ya gabatar da abubuwa 27 da aka gano a binciken mutuwar Janar Attahiru a jirgin sama

  • AIB sun mika rahoton farko na binciken hadarin jirgin da ya kashe COAS a Kaduna
  • Wannan bincike ya fito bayan kwanaki kusan 115 da mutuwar Janar Attahiru Ibrahim
  • A watan Mayu jirgin sama ya kashe tsohon hafsun sojojin kasa da wasu jami’ai tsaro

Abuja - Kwamitin da aka kafa domin ya yi bincike a kan hadarin jirgin saman da ya kashe tsohon hafsun sojojin kasa, Ibrahim Attahiru ya gama aikinsa.

Jaridar Punch tace kwamitin ya gabatar da rahoton farko ga rundunar sojojin saman Najeriya. Rahoton wannan bincike ya bankado wasu abubuwa 27.

Mai magana da yawun bakin rundunar sojojin sama, Edward Gabkwet da kakakin AIB, Tunji Oketunbi sun bayyana haka a wani jawabi da suka fitar.

Rahoton binciken ya fito ne bayan sama da watanni uku da mutuwar hafsun sojojin kasa, Laftana-Janar Attahiru Ibrahim da wasu sojoji a Kaduna.

Kara karanta wannan

Sojoji sun damke tsohon soja yana jigilar tulin wiwi da kwayoyi daga Ondo zuwa Jihohin Arewa

Vanguard tace an yi wa jawabin take da 'Accident Investigation Bureau Submits Interim Report On Aircraft Accident Involving Nigerian Air Force King Air-350 Aircraft To The Chief Of Air Staff’.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Janar Attahiru I.
Marigayi Attahiru Ibrahim Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Gutsuren jawabin da aka fitar

"Bayan kusan watanni uku ana bincike, Shugaban AIB, Injiniya Akin Olateru FNSE ya gabatar da rahoton abin da ya faru ga shugaban hafsun sojojin sama, Air Marshal I. Amao, a yau, ranar 15 ga watan Satumba, 2021, a ofishinsa da ke hedikwatar NAF a Abuja."
"An kasa rahoton zuwa bangare-bangare; bayanan da aka samu wajen binciken, abin da aka fahimta daga bayanan da aka samu, da kuma kammala wa, wanda ya kunshi abin da aka gano da shawarwari."
“A somin-tabin binciken, an gano abubuwa 27 da shawarwari 8 da ya kamata ayi gaggawar dauka.”

Kara karanta wannan

Jerin fitattun 'yan Najeriya 4 da Buhari zai iya nadawa a matsayin sabon ministan noma

Wannan ne karon farko da AIB suka yi irin wannan bincike

Kwamitin na AIB ne aka ba dama ya gudanar da wannan bincike duk da cewa bai da hurumin ya gudanar da bincike game da hadarin jiragen sojojin kasa.

Kamar yadda jawabin ya bayyana, ana sa rai rahoton karshe zai kunshi cikakken bayanin abin da ya faru da kuma matakan da ya kamata a dauka nan gaba.

Attahiru ya yi mutuwar Akahan

A wani rahoto da muka fitar a lokacin da abin ya faru, kun ji cewa Janar Attahiru ne mutum na biyu da ya mutu kan wannan kujera sakamakon hadarin jirgi.

Na farko da ya mutu shine Laftanan Kanal Joseph Akahan wanda yake rike da mukamin shugaban hafsoshin soji a lokacin da ake yakin basasa a 1968.

Asali: Legit.ng

Online view pixel