Za ayi zazzaga a APC, Jam’iyya za ta koma fatattakar wadanda suka yi mata taurin-kai

Za ayi zazzaga a APC, Jam’iyya za ta koma fatattakar wadanda suka yi mata taurin-kai

  • Uwar APC za ta hukunta wadanda suke kai karar Jam’iyya gaban Alkali
  • Wani jigon jam’iyyar yace sun gaji da surutu, za su fara daukar matakai
  • APC NEC ta umarci ‘ya ‘yan jam’iyya suyi sulhu a gida, a guji zuwa kotu

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC za ta dauki mataki mai tsauri a kan ‘ya ‘yanta da suka saba wa umarnin da aka bada na yin sasanci, suka je kotu.

Jaridar Punch tace jam’iyyar APC mai mulki za ta dauki mataki a kan duk wadanda suka shigar da kara a maimakon a zauna ayi sulhun cikin-gida.

Wani daga cikin manyan jam’iyyar a Abuja ya shaida wa jaridar cewa za a dauki wannan mataki.

Za a ga aiki da cika wa

Kara karanta wannan

‘Yan bindigar da suka yi garkuwa da magidanci da iyalinsa 4 a Kaduna sun nemi a biya naira miliyan 20

A cewar wannan babba da ba a bayyana wanene shi ba, jam’iyyar APC za ta dauki mataki a kan masu saba mata a maimakon ta cigaba da ja masu-kunne.

“Mun tashi daga yin barazana, za mu fara daukar mataki.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban APC
Shugaban APC, Gwamna Mai Mala Buni Hoto: Maistrategy
Asali: Facebook

Uwar jam’iyya za ta dauki matakin da bai saba tsarin mulkinta ba. Za a karfafa wa shugabannin jam’iyya da ke jihohi su hukunta duk masu kunnen-kashi.

“A matakin jam’iyya na kasa muna tattara wadanda suka saba doka da abubuwan da suka faru. An ba reshen jam’iyya na jiha karfi su dauki matakin da ya dace, wanda ya zo daidai da doka da tsarin jam’iyyar APC.”

Rikicin Enugu ya cabe

Rahoton yace uwar jam’iyyar za ta dauki wannan mataki ne a lokacin da reshen APC na Enugu ya kicibe da rikicin cikin gida saboda sabanin da ake ta samu.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan sanda ke 'tatsar' jama'a kafin su bibiyi miyagun da suka sace 'yan uwansu

Majalisar amintattu ta jam’iyyar APC da za a kaddamar a karkashin Janar Joseph Okoloagu mai ritaya tayi fatali da korar da ake cewa an yi wa Ben Nwoye.

Kwanakin baya aka ji wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar APC na jihar Enugu sun kori Ben Nwoye. Daga baya ‘yan sanda suka je har sakatariyar jam’iyya suka kama shi.

Ibo suna harin 2023

A yau kun ji cewa an samu labarin wasu mutum 18 da wata kungiyar kabilar Ibo a fitar a matsayin wadanda za su iya tsaida wa takarar shugaban kasa.

Cikin jerin da aka fiar akwai gogaggun ‘Yan siyasan APC da PDP. An samu Ministoci, Sanatoci da Gwamnoni masu ci yanzu da wadanda suka yi mulki a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel