Zaben 2023: Hon. Elumelu ya bayyana Gwamnan da zai iya hambarar da APC daga kan mulki

Zaben 2023: Hon. Elumelu ya bayyana Gwamnan da zai iya hambarar da APC daga kan mulki

  • Ndudi Elumelu ya roki Ifeanyi Okowa ya nemi kujerar Shugaban kasan Najeriya
  • ‘Dan Majalisar yace Gwamnan Deltan zai iya yin waje da Gwamnatin APC a 2023
  • Hon. Elumelu ya zargi gwamnatin APC da kashe kasa da kuma raba kan jama'a

Delta - Shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai, Ndudi Elumelu ya roki gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa ya nemi takarar shugaban kasan 2023.

Honarabul Ndudi Elumelu yace gwamna Ifeanyi Okowa zai iya ceto Najeriya daga halin da jam’iyyar APC mai mulki ta jefa al’ummar kasar nan.

‘Dan majalisar yake cewa Okowa zai iya kawo zaman lafiya, hadin-kai da bunkasar tattalin arziki.

Jaridar This Day tace Elumelu ya yi wannan bayani ne wajen rantsar da sababbin shugabanni na wata kungiyar mutanen garin Asaba da ke jihar Delta.

Jagoran ‘yan adawa na majalisar wakilan ya koka game da yadda gwamnatin APC ta kashe kasa, a cewarsa APC ba ta san aiki ba, kuma ta raba kawuna.

Kara karanta wannan

Ba tsaro a Najeriya, sai zubar da jini ake, inji Sule Lamido yayin ganawa da Obasanjo

A shekaru shida a mulki, Ndudi Elumelu yace APC ta kawo kashe-kashe, ta’addanci, tabarbarewar abubuwan more rayuwa, talauci da matsin tattalin arziki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zaben Edo
Gwamna Okowa wajen kamfe Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Meyasa ake mara wa Okowa baya

"Idan Ifeanyi Okowa ya dare kan mulkin kasar nan, zai yi wa Najeriya irin ayyukan da aka gani a Delta."
“Abubuwa ba su taba tabarbarewa haka ba a tarihin kasar nan. Saboda haka ina kira ga ‘yan Najeriya su hada-kai, su yi waje da APC.”
“Ina yabon Gwamna Okowa na ayyukan jajircewa da ya yi inda aka ga abubuwan more rayuwa a jiharmu, kuma rayuwar mutane ta kara dadi.”
“Daukacin mutanen Delta da ma Najeriya sun yi dace da Okowa. Na yi imani yana da abin da ake bukata wajen shawo kan matsalolin kasar nan.”

An rahoto Elumelu yana kira ga Okowa ya fito takarar shugaban kasa domin ya bauta wa Najeriya.

Kara karanta wannan

Buhari: Gwamnan Ebonyi ya yi wa Wike raddi, ya fallasa wadanda suka kawo matsalar tsaro

APC za ta yi nasara a 2023?

Gwamnan Katsina, Aminu Masari ya fadi abin da zai sa Jam’iyyar su ta ci zabe, su koma kan mulki a 2023, yace APC za a lashe zabe da kuri'u miliyan 30.

Ganin APC ta shirya zabukan shugabanni lafiya lau a Katsina, shiyasa Masari ya fara cika-baki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel