Gwamnan Zamfara Matawalle Zai Farfaɗo Da Rundunar ‘Yan Sa Kai’ Don Kawar Da Ta’addanci a Jihar

Gwamnan Zamfara Matawalle Zai Farfaɗo Da Rundunar ‘Yan Sa Kai’ Don Kawar Da Ta’addanci a Jihar

  • Gwamnatin jihar Zamfara zata farfado da rundunar tsaron farar hula ta hadin guiwa (CJTF) wacce aka fi sani da “Yan sa kai”
  • Gwamnatin za ta farfado da rundunar ne don yaki da ‘yan ta’addan jihar kamar yadda shugaban kwamitin tsaron jihar ya bayyana
  • Abdullahi Shinkafi ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Gusau yayin tattaunawa da manema labarai

Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara za ta farfado da kungiyar hadin guiwa ta tsaro na farar hula ta CJTF wacce aka fi sani da “Yan sa kai” don kawo tallafi ga jami’an tsaron jihar akan ‘yan ta’addan da suka addabi Zamfara, rahoton Premium Times.

Shugaban kwamitin tsaro da yanke hukunci ga ‘yan bindiga na jihar Zamfara, Abdullahi Shinkafi, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da NAN tayi da shi a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jam'iyyar APC ta fatattaki tsohon gwamna da wasu mambobi 40

Gwamnan Zamfara Matawalle zai dawo da 'Ƴan Sakai', Majiyar Gwamnati
Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Gwamnatin jihar ta yanke shawarar ne don kawo karshen duk wasu ‘yan ta’adda da ke jihar

Kamar yadda Premium Times ta ruwaito, Shinkafi, wanda shi ne mai bai wa gwamna Bello Matawalle shawarwari a harkar gwamnati ne ya ce:

“Gwamnatin jihar ta yanke wannan shawarar ne bisa ganin yadda ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane suke ci gaba da yawaita a fadin jihar.
“Gwamnatin za ta yi hakan bisa wani sabon sharadi. Wajibi ne duk mai neman shiga kungiyar ‘Yan sa kai’ zai gabatar da mutane 3 su kasance tsayayyu a gare shi kafin a jaddada shi.”
“Za a farfado da rundunar Yansakai don taimako ga jami’an tsaro wurin ganin karshen duk wasu ‘yan bindiga da masu basu bayanai."

Premium Times ta ruwaito yadda Shinkafi ya nemi taimakon rundunar don yaki da rashin tsaro a fadin jihar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin jihar Katsina ta fitar da sabbin kalolin fentin ababen hawa na haya a fadin jihar

Shinkafi ya yaba wa mazauna jihar akan juriyar su

“Mun yaba wa mazauna jihar bisa hakuri, addu’o’i, juriya da karfin guiwar da suke bayarwa ga sababbin dokokin tsaron da jihar ta kafa don kawo karshen ta’addanci da garkuwa da mutane.
“Yanzu haka jami’an tsaro sun samu tarin nasarori sakamakon luguden wutar da sojin kasa da na sama suke yi wa ‘yan ta’adda,” a cewarsa.

Mai bai wa gwamnan shawara ya bayyana yadda gwamnatin tarayya ta dakatar da hanyoyin sadarwa a jihar Zamfara da sauran hanyoyin tallafa wa tsaro duk don kakkabo duk wasu ‘yan ta’adda a jihar Zamfara.

"Rufe kasuwannin shanu ma tana daya daga cikin matakan da gwamnatin jihar ta dauka sakamakon yadda ‘yan ta’addan suke kasuwancin miyagun makamai da shanu,” kamar yadda ya ce.

Shinkafi ya yaba wa Gwamna Matawalle akan sababbin hanyoyin da gwamnatin sa ta dauka don yaki da duk wasu ta’addanci a jihar.

A cewar sa, yanzu haka jami’an tsaro sun ragargaji ‘yan ta’adda da dama da ke fadin jihar.

Kara karanta wannan

Sabuwar doka: Gwamnatin jihar Jigawa ta sanya dokar hana babur a fadin jihar

Adamawa: Jarumin mai shago ya ragargaji ‘yan daba 2 da su ka yi kokarin fasa masa shago

A wani rahoton, kun ji wani mai shago, Mohammed Hamman Adama, ya nuna gwarzontakarsa bayan ya yi dambe da wasu yaran Shila yayin da su ka yi kokarin balle masa shagon sa da ke Sangere Bode a karamar hukumar Yola ta kudu a jihar Adamawa.

LIB ta ruwaito yadda aka tattaro bayanai akan wadanda ake zargin, Umar Sa’ad, mai shekaru 18 da Mohammed Idris, mai shekaru 20 suka lallaba shagon sa da misalin karfe 2:00 na daren 2 ga watan Satumban 2021 da addunan su, gudumomi, sanduna da sauran miyagun makamai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel