An Bindige Kwamandan 'Yan Sakai Yayin Musayar Wuta Da 'Yan Bindiga a Kogi

An Bindige Kwamandan 'Yan Sakai Yayin Musayar Wuta Da 'Yan Bindiga a Kogi

  • Fitaccen kwamandan ‘yan sa kai, Alhassan Alhassan ya rasa ran sa sakamakon musayar wutar da suka yi da masu garkuwa da mutane a wani daji a jihar Kogi
  • Daya daga cikin ‘yan sa kan ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da misalin karfe 11:23 na safe a daji a anguwar Tanahu dake karamar hukumar Kogi a jihar
  • Kamar yadda rahotanni suka bayyana, saboda yadda suka addabi kauyakun ne yasa kwamandan ya jagoranci yaran sa zuwa dajin

Jihar Kogi - Wani fitaccen kwamandan ‘yan sa kai, Alhassan Alhassan, ya rasa ran sa sakamakon musayar wutar da suka yi da masu garkuwa da mutane a dajin kauyen Tanahu dake masarautar Gegu-Beki a karamar hukumar Kogi a jihar.

Kara karanta wannan

Masu garkuwa da mutane sun mamaye kauyen Abuja, sun sace matan aure 2

Daya daga cikin ‘yan sa kan wanda ya bukaci a boye sunan sa ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da misalin karfe 11:23 na safe., Daily Trust ta ruwaito.

An Bindige Kwamandan 'Yan Sakai Yayin Musayar Wuta Da 'Yan Bindiga a Kogi
'Yan Bindiga. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar sa kwamandan ya jagoranci yaran sa zuwa dajin don su fuskanci masu garkuwa da mutanen sakamakon yadda suka addabi kauyakun Aduho da Tanahu na yankin.

Masu garkuwa da mutanen sun boye ne bayan sun hango ‘yan sa kai.

Daily Trust ta ruwaito yadda ya ce masu garkuwa da mutanen sun boye ne bayan sun ga ‘yan sa kan suna shiga cikin dajin sannan suka fara harbe-harbe ko ta ina.

Ya ce:

“Duk da harbin da suke yi, kwamandan da yaran sa ma suna ta musayar wuta har sai da harsashin bindigan daya daga cikin su ya sami cikin sa.”

Kara karanta wannan

Adamawa: Jarumin mai shago ya ragargaji ‘yan daba 2 da su ka yi kokarin fasa masa shago

A cewarsa daga nan kwamandan ya fadi kasa bayan harsashin ya same shi , duk da dai harsashin ya sami wasu masu garkuwa da mutanen.

Dama kwamandan dan asalin Toto ne a jihar Nasarawa

Bisa ruwayar Daily Trust, an dauki gawar mamacin an kai shi kauyen shi (Toto) dake jihar Nasarawa inda aka yi jana’izar sa kamar yadda musulunci ya tanadar.

Daily Trust ta ruwaito yadda sanannen shugaban ‘yan sa kan ya jagoranci wani farmaki da suka kai wa masu garkuwa da mutane a titin Toto zuwa Umaisha a jihar Nasarawa sakamakon yadda suka addabi matafiya masu bin hanyar.

Onyiwo na Gugu- Beji, Alhaji Mohammed Abba Suleiman, ya tabbatar da yadda lamarin ya faru bayan manema labarai sun kira shi ta waya don jin ta bakin sa akan mutuwar.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kogi, CSP Williams Ovye Aya, bai dauki wayar wakilin Daily Trust ba sannan bai mayar da ansa ga sakon da aka tura masa ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tare motar jigon PDP sun yi awon gaba da shi da direbansa

Adamawa: Jarumin mai shago ya ragargaji ‘yan daba 2 da su ka yi kokarin fasa masa shago

A wani rahoton, kun ji wani mai shago, Mohammed Hamman Adama, ya nuna gwarzontakarsa bayan ya yi dambe da wasu yaran Shila yayin da su ka yi kokarin balle masa shagon sa da ke Sangere Bode a karamar hukumar Yola ta kudu a jihar Adamawa.

LIB ta ruwaito yadda aka tattaro bayanai akan wadanda ake zargin, Umar Sa’ad, mai shekaru 18 da Mohammed Idris, mai shekaru 20 suka lallaba shagon sa da misalin karfe 2:00 na daren 2 ga watan Satumban 2021 da addunan su, gudumomi, sanduna da sauran miyagun makamai.

Bayan isar su shagon har sun fara balle kofar don su samu nasarar yasar shagon. Su na kici-kicin balle kofa mai shagon ya ji kara ya fita cikin sauri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel