Da dumi-dumi: Gwamnatin jihar Rivers ta kai gwamnatin tarayya kotun koli kan harajin VAT
- Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya garzaya kotun kolin Najeriya
- Sama da mako guda kenan ana kai ruwa rana kan lamarin harajin VAT
- Yayinda hukumar FIRS ke ganin hakkinta ne, gwamnoni sun ce sam ba zasu yarda ba
Abuja - Antoni Janar na Gwamnatin jihar Rivers ya garzaya kotun kolin Najeriya domin bukatar ayi watsi da hukuncin kotun daukaka kara da ta dakatar da ita daga fara karban harajin VAT.
Zaku tuna cewa hukumar FIRS ta shigar da kara kotun daukaka kara domin hana jihar Rivers da sauran jihohin Najeriya aiwatar da sabbin dokokin karbar harajin VAT da suka samar.
Kotun daukaka kara ta hana jihar Rivers karbar kudin harajin VAT
Kotun daukaka kara dake Abuja ta dakatad da gwamnatin jihar Rivers karbar kudin harajin VAT da hukumar FIRS ta saba karba.
A zama na farko, Alkali Haruna Simon Tsanami ya yanke ranar Juma'a, ya bada umurnin cewa ayi watsi da sabuwar dokar da majalisar wakilan jihar Rivers ta kafa kuma gwamnan Wike ya rattafa hannu.
Jihar River ta garzaya kotun koli
Martani kan hukuncin kotun daukaka kara, jihar Rivers a takardar da ta shigar kotun koli kuma Vanguard ta shaida ranar Talata, ta bukaci a canza Alkalan da ke zaune kan karar yanzu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dokar VAT za ta iya talauta Jihohi 30, Gwamna Wike yace sai dai sama da kasa su hade
Jihohi da-dama a Najeriya ba za su iya sauke nauyin da ke kansu ba domin gwamnatin tarayya za ta rasa kaso na abin da take samu daga haraji daga wajen gwamnatin tarayya ba.
Mafi yawan jihohi sun dogara ne da kason da suke samu daga asusun hadaka na FAAC saboda gwamnoninsu ba su samun kudin-shiga.
Jihohin Ribas da Legas ne suke tattara 70% na harajin kayan masarufi a Najeriya, amma a karshe ana raba kudin ne tare da sauran gwamnonin jihohi 36.
Gwamnan Ribas, Nyesom Wike da ya shigar da kara a kotu ya dage a kan bakararsa, yace ko sama da kasa za su hade ba zai bar FIRS ta karbi harajinsu ba.
Asali: Legit.ng