Da duminsa: Kotun daukaka kara ta hana jihar Legas da Rivers karbar kudin harajin VAT

Da duminsa: Kotun daukaka kara ta hana jihar Legas da Rivers karbar kudin harajin VAT

  • Kotu ta umurci FIRS, Gwamnatin Legas da Gwamnatin Rivers kada su saka magana kan lamarin VAT
  • Gwamnatin Rivers ta shirya tsaf don fara karban harajin VAT daga kamfanonin dake jihar
  • Ba tare da bata Lokacin ba jihar Legas ta kafa sabuwar doka don yin haka itama

Kotun daukaka kara dake Abuja ta dakatad da gwamnatocin jihar Rivers da Legas daga karbar kudin harajin VAT da hukumar FIRS ta saba karba daga hannun kamfanoni.

A hukuncin da Alkali Haruna Simon Tsanami ya yanke ranar Juma'a, ya bada umurnin cewa ayi watsi da sabuwar dokar da majalisar wakilan jihar Rivers ta kafa kuma gwamnan Wike ya rattafa hannu, rahoton DailyTrust.

Hakazalika majalisar dokokin Legas ta samar da irin wannan doka.

Amma hukuncin kotun daukaka kara ta fito yayinda gwamnan Legas, Babajide Sanwoolu, ke shirin rattafa hannu kan na Legas.

Kara karanta wannan

Gwamnatin jihar Katsina ta fitar da sabbin kalolin fentin ababen hawa na haya a fadin jihar

Hukumar samar da kudin shiga na Najeriya FIRS ta shigar da kara kotun daukaka kara kan hukuncin da wata kotu a Fatakwal ta yanke na halastawa jihohi karban harajin VAT.

Kotun na Legas a baya ta haramtawa hukumar FIRS da Antoni Janar na tarayya daga karban kudin harajin VAT daga wajen mazauna jihar Legas.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da duminsa: Kotun daukaka kara ta hana jihar Legas da Rivers karbar kudin harajin VAT
Da duminsa: Kotun daukaka kara ta hana jihar Legas da Rivers karbar kudin harajin VAT
Asali: Original

Dokar VAT za ta talauta Jihohi 30, Gwamna Wike yace sai dai sama da kasa su hade

Jihohi da-dama a Najeriya ba za su iya sauke nauyin da ke kansu ba domin gwamnatin tarayya za ta rasa kaso na abin da take samu daga harajin VAT.

Baya ga hukuncin da kotu ta yi inda ta ba jihohi damar karbar harajinsu, gwamnatin Najeriya tana fama da matsalar karancin kudin-shiga a halin yanzu.

Daily Trust tace mafi yawan jihohi sun dogara ne da kason da suke samu daga asusun hadaka na FAAC saboda gwamnoninsu ba su samun kudin-shiga.

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban kasa ta saki hotunan ziyarar da Buhari ya kai Owerri, jihar Imo

Jihohin Ribas da Legas ne suke tattara 70% na harajin kayan masarufi a Najeriya, amma a karshe ana raba kudin ne tare da sauran gwamnonin jihohi 36.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng