‘Yan bindiga sun sake kashe mutane 12, sun raunata wasu Bayin Allah a Kaduna
- ‘Yan bindiga sun kai hari a garin Zangon-Kataf, sun hallaka mutane da-dama
- Yayin da mutane 12 suka bakunci barzahu, akwai mutane biyu da suke jinya
- Gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da harin, tace jami'an tsaro suna bincike
Kaduna - Wasu ‘yan bindiga sun kai hari har sun kashe mutane 12, sannan sun jikkata mutane biyu a kauyen Peigyim a kusa da Kibori a yankin Zangon Kataf.
Daily Post tace kwamishinan harkoki da tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Litinin, 13 ga watan Satumba, 2021.
Su wanene wadanda suka mutu?
Samuel Aruwan ya bada sunayen wadanda aka kashe; Philbia Ysuaf, Suzanna Ezekiel, Rahib Alex, Ishaku Bamaiyi, Deborah Ishaku, Tinat Bamaiyi, da Zichat Kefas.
Ragowar sune Sunday Daniel, Hauwa Gabriel, Fedelia Famson, Sadia Donald, da Goodness Kefas.
Tribune tace wadannan miyagun mutane sun shiga Zangon Kataf sun hallaka mutane ne a ranar Lahadi da yamma, suka bar mutane suna makokin 'yanuwansu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mai girma Kwamishinan yace akwai wasu mutane biyu da suka samu rauni da yanzu ake jinyar su.
Aruwan bai bayyana sunayen wadanda suke jinya ba, amma yace gwamnati za ta yi bincike domin a gano wadanda ke da hannu a wannan ta’addancin.
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya karbi rahoton harin da aka kai a karamar hukumar ta Zangon Kataf, ya aika ta’aziyyarsa ga wadanda abin ya shafa.
A jawabinsa, Malam El-Rufai ya roki Ubangiji ya jikan wadanda suka riga mu gidan gaskiya, sannan yana fatan samun waraka ga wadanda suka samu rauni.
Jaridar tace gwamna El-Rufai ya yi alkawari jami’an tsaro za su karada yankunan yayin da ake bincike domin a gano wadanda suka yi wannan danyen aikin.
An kai hari a Zaria
A karshen watan jiya ne aka ji cewa 'yan bindiga sun afka unguwar Zango da ke kusa da Samarun Zaria a jihar Kaduna sun sace a kalla mutane bakwai.
Wani shaidan gani da ido ya ce maharan sun afka unguwar ne da tsakar dare a lokacin mutane suna barci. 'Yan bindigan sun kashe wata mata da suka dauke.
Asali: Legit.ng