Jam'iyyar APC ta kafa kwamitin dinke barakar dake cikinta

Jam'iyyar APC ta kafa kwamitin dinke barakar dake cikinta

  • Yayinda ake shirin zaben gangamin jam'iyyar, za'a dinke barakar dake cikin jam'iyyar
  • A ranar Litnin, uwar jam'iyyar ta fitittiki mutum sama da 50 daga jam'iyyar
  • Mambobin jam'iyyar a fadin tarayya sun shigar da kararraki kan juna kotu

Abuja - Kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar All Progressives Congress APC ta kasa a ranar Talata ta kafa kwamitin sulhu tsakanin 'yayan jam'iyyar a fadin tarayya.

Mambobin kwamitin sun hada da tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu; Ministan harkoki na musamman, George Akume; tsohon gwamnan jihar Enugu, Sullivan Chime, dss.

Hakan na kunshe cikin jawabin da jam'iyyar ta saki mai taken, 'APC Shugaban CECPC ya nada Adamu, Akume, Dogara, Chime, Adebule, dss cikin kwamitin sulhu tsakanin 'yayan jam'iyya,'.

Jawabin na dauke da sanya hannun sakataren jam'iyyar ta kasa John Akpanudoedehe, rahoton ThePunch.

Kara karanta wannan

Tsohon Dan Majalisar Dokoki da Wasu Mambobin Jam'iyyar Adawa Sun Sauya Sheka Zuwa APC

Jam'iyyar APC ta kafa kwamitin dinke barakar dake cikinta
Jam'iyyar APC ta kafa kwamitin dinke barakar dake cikinta Hoto: APC
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani sashen jawabin yace:

"Shugaban kwamitin rikon kwaryan jam'iyyar All Progressives Congress APC, Gwamna Mai Mala Buni ya amince da sunayen yan kwamitin sulhu a jam'iyyar ta kasa."
"Sunayen sune Sen. Abdullahi Adamu – Shugaba; Otunba Moses Alake Adeyemo – Sakatare, Sen. George Akume; H.E. Sullivan Chime; H.E. Ali Saad Birnin kudu; Rt. Hon. Yakubu Dogara; Alh.Suleiman Argungu; Dr. Mrs. Oluranti I. Adebule; da Dr. Mrs. Beta Edu."

Jam'iyyar APC Ta Sanar da Ranar Gangamin Taronta na Jihohi

Kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya bayyana ranar da za'a gudanar da tarukan jam'iyya a matakin jihohi, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Kwamitin ya sanar da cewa za'a gudanar da gangamin tarukan APC a matakin jihohi ranar Asabar, 2 ga watan Oktoba, inda za'a zabi shugabannin APC a jihohi.

Kara karanta wannan

Jiga-jigan APC sama da 30 suna harin kujerar Ministan wutan lantarki da aka tsige

Wannan na kunshe ne a wani gajeren jawabi da sakataren kwamitin rikon kwarya na APC ta kasa, Sanata John James Akpanudoedehe, ya fitar ranar Litinin a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel