Ba zan lamunci uzirin kowa ba, COAS ya sanar da kwamandojin dakarun soji

Ba zan lamunci uzirin kowa ba, COAS ya sanar da kwamandojin dakarun soji

  • COAS Laftanal Janar Faruk Yahaya ya ja kunnen kwamandojinsa kan cewa ba zai lamunci uziri daga kowa ba
  • Ya sanar da cewa ya zama dole kwamandojin su kasance sahun gaba wurin tabbatar da nasarar ayyukan yaki da ta'addanci
  • COAS Yahaya ya ce hukuma na cigaba da samar wa da dakarun kayan aiki tare da share musu duk wani kuka na su

FCT, Abuja - Shugaban dakarun sojin kasa, COAS Faruk Yahaya ya ja kunnen cewa ba zai lamunci uziri daga kwamandojin da ke jagorantar dakarun soji ba a filin daga da kuma yakar matsalar tsaron da kasar nan ke fuskanta ba.

Yahaya ya bada wannan wannan jan kunnen a yayin bude wani taro kashi na biyu da na uku na sojin da da ake hade a ranar Litinin a Abuja, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Masallacin kasa ya kaddamar da asusun neman tallafin N29bn na ayyuka

Ya ce rundunar da ke karkashinsa za ta cigaba da mayar da hankali tare da kokarin ganin ana samun cigaba wurin yakar matsalolin da ake ciki.

Ba zan lamunci uzirin kowa ba, COAS ya sanar da kwamandojin dakarun soji
COAS Laftanal janar Faruk Yahaya ya ce ba zai karba uzirin kowanne kwamanda ba. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

COAS ya bayyana cewa ya umarci dukkan sojoji da ke ayyukan samar da zaman lafiya da su cigaba da aikin da suke yi tare da karawa, Daily Nigerian ta wallafa.

Ya kara da cewa, ya umarci dukkan ayyukan da ake na musamman ballantana a yankin arewa ta tsakiya da arewa maso yamma da su cigaba domin shawo kan matsalar tsaron yankunan.

"A don haka, dole ne kwamandoji su tabbatar da sun cigaba da ayyukansu tare da cigaba da tsananta su har sai an cimma manufa.
"Dole ne kwamandoji su fito da dabaru kuma mabiyansu su dauka, dole ne a dauka mataki cin galaba kan dukkan kalubale ba tare da duban yankunan ba.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan yari, sun saki fursunoni 240 sannan suka kashe sojoji a Kogi

“Ba zan lamunci wani uziri daga kowa ba. Rashin nasara har abada rashin nasara ce, ba ta duban halin da ake ciki," yace.

Yahaya ya ce ana cigaba da kokarin samarwa sojojin kayan aiki domin inganta ayyukansu. Ya ce ana cigaba da kokarin ganin cewa an dakatar da matsalar tashin bama-bamai wanda ya zama babbar matsala ga dakarun da kuma ayyukansu a arewa.

Kebbi: Iyayen daliban FGC Yauri sun cire rai gwamnati za ta karbo musu 'ya'yansu

A wani labari na daban, iyayen daliban da aka sace na makarantar kwalejin tarayya da ke Birnin Yauri a jihar Kebbi sun ce sun fitar da ran cewa gwamnati za ta karbo musu 'ya'yansu da aka sace.

A halin yanzu, daliban sun kwashe kwanaki 87 a hannun miyagun da suka sace su, Daily Trust ta ruwaito.

'Yan bindiga kusan 150 sun kutsa makaranta a tsakar rana kuma sun yi awon gaba da dalibai sama da 90 tare da malaman makarantar.

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

Asali: Legit.ng

Online view pixel